Gwamnatin Trump ta janye jami’an farin kaya da ke gadin Kamala Harris

Spread the love

Shugaba Trump na Amurka Donald Trump ya janye masu tsaron tsohuwar mataimakiyar shugaban Amurka a zamanin Joe Biden, Kamala Haris da shugaba Joe Biden ya ba ta, kamar yadda wani daga cikin masu ba ta shawara ya tabbatar.

Bisa doka dai a matsayin Kamala na tsohuwar mataimakiyar shugaban ƙasa, ta cancanci samun tsaro na tsawon watanni shida bayan barin mulki a watan Janairu wanda ya kamata ya ƙare a watan Yuli.

Tshohon shugaba Joe Biden ya tsawaita lokacin tsaron ga mataimakiyarsa da shekara guda to amma yanzu shugaba Trump ya janye ƙarin a wata takarda da aka yi ranar Alhamis, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Janye jami’an tsaron dai na zuwa ne kafin Harris ta fara wani rangadi da manufar tallata littafinta da ta rubuta mai suna “104 Day” da ke bayani kan rayuwar gangamin yaƙin neman zaɓenta a 2024.

Waɗansu majiyoyin da suke da masaniya da al’amarin sun shaida wa CBS, cewa babu wata barazana a baya-bayan nan ga Kamala Harris da ke buƙatar a ƙara tsawaita mata kariya daga wanda ta samu na tsawon watanni shida.

A shekarar 2008 ne majalisar dokokin Amurka ta yi dokar da ke baiwa jami’an tsaron farin kaya su bai wa tsoffin mataimakan shugaban ƙasar Amurka da iyalansu kariya bayan barin ofis.

Yanzu watanni bakwai kenan da barin Kamala Harris ofis bayan kammala wa’adinsu a watan janairu.

Kariya ga mijin Harris, Doug Emhoff ya kare a ranar 1 ga watan Yuli kamar yadda doka ta tanada.

Yanzu Kamala Harris za ta rasa jami’an da aka bata domin bata kariya da kadarorinta a Los Angeles da ma duk wani matakin tsaro da za a iya ɗauka wajen daƙile barazanar da ka iya taso mata.

Gwamnonin California da magajin garin Los Angeles dukkanninsu sun bayyana takaici, kamar yadd BBC Hausa ta ruwaito.

By Babaji