Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ya amince cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai magance matsalar wutar lantarki a Nijeriya ba, duk da alƙawarin da ya yi wa ’yan ƙasa kafin zaɓen 2023.
Sai dai kwamitin ya ce gwamnatin Tinubu na ci gaba da ƙoƙarin magance matsalolin da suka dabaibaye ɓangaren wutar lantarki domin samar da ingantacciyar wuta a ƙasar.
Mai magana da yawun kwamitin, Dele Alake, ya bayyana cewa gyaran ɓangaren wutar lantarki na ci gaba da gudana.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Alake ya ce gwamnati na ɗaukar matakai domin magance matsalolin kuɗi da na tsari da suka addabi ɓangaren wutar lantarki.
Ya ce Tinubu ya sanya hannu kan Dokar Wutar Lantarki ta 2023, ƙasa da makonni biyu bayan hawansa mulki, matakin da ya bai wa gwamnatocin jihohi damar samarwa da rarraba wutar lantarki a jihohinsu.
A cewarsa, jihohi da suka haɗa da Legas, Enugu, Abiya, Oyo, Kaduna da Neja sun fara amfani da dokar wajen inganta harkokin wutar lantarki.
Alake ya kuma ce gwamnatin Tinubu ta gaji bashin da ya haura Naira tiriliyan shida a ɓangaren wutar lantarki, inda ta ƙaddamar da shirin bayar da lamunin Naira tiriliyan huɗu domin biyan basukan kamfanonin samar da wutar lantarki da na iskar gas.
Ya ƙara da cewa sama da kwastomomi miliyan 1.5 ne suka samu mitocin wutar lantarki ta hanyar Shirin Samar da Mitocin Wutar Lantarki na Shugaban ƙasa cikin shekaru uku.
Ya ce gwamnati na kuma zuba jari wajen gina sabbin tashoshin wutar lantarki, inganta hanyoyin sadarwa da samar da wutar hasken rana ga al’ummar karkara, jami’o’i da asibitoci.
Alake ya bayyana cewa wasu daga cikin ayyukan za su ɗauki lokaci kafin a kammala su saboda suna buƙatar kayan aiki na musamman da kuma manyan ayyukan gine-gine.
Ya jaddada cewa Tinubu bai yi watsi da alƙawarinsa na magance matsalar wutar lantarki ba.
Ya kuma ce gwamnati za ta gabatar wa ’yan ƙasa da nasarorin da ta samu, tare da bayyana matsalolin da har yanzu ba a shawo kansu ba gabanin zaɓen 2027.
A cewarsa, inganta samar da wutar lantarki aiki ne da ke gudana, yayin da gwamnati ke ƙoƙarin daidaita farashin wutar da kuma kare muradun masu amfani da ita.
