Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mutum 22 sun gamu da ajalinsu, yayin da wasu 20 suka jikkata, bayan wata babbar mota da ta yi lodin mutane da dabbobi ta yi hatsari a kan hanyar Lambata zuwa Lapai da ke Jihar Neja.
Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Litinin.
Motar ta taso daga Kano zuwa Legas ne lokacin da hatarin ya auku da misalin ƙarfe 3 na safe, sakamakon gudun wuce ƙima.
Hukumar Kiyaye Haɗura ta ƙasa (FRSC), ta ce dukkanin fasinjojin da ke cikin motar maza ne.
An kai gawarwakin Babban Asibitin Suleja, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Gwamnati na Lambata.
Daga baya, iyalan wasu daga cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su, sun ɗauke su zuwa wasu cibiyoyin lafiya.
Jama’a sun ce hatsarin mota na ci gaba da zama ruwan dare a hanyar Lambata zuwa Bida, musamman manyan motocin dakon kaya da ke ɗauko mutane da dabbobi a lokaci guda.
Wasu sun ɗora laifi kan lalacewar hanya, gudun wuce ƙima da rashin bin dokokin hanya.
Aƙalla mutum 80 ne suka rasu a wannan hanya cikin shekarar da ta gabata.
Wasu mazauna yankin sun ce hanyar tana hatsari sosai ga ƙananan motoci da masu babura, saboda yawan manyan motoci da ke zirga-zirga a hanyar.
Sun buƙaci gwamnati da ta gyara hanyar, tare da ɗaukar mataki kan direbobi masu ganganci.
Ana ci gaba da aikin gyaran hanyar Lambata-Lapai-Agaie-Bida ƙarƙashin wani shiri na NNPC.
Amma sai an kammala aikin da kuma kafa dokoki masu tsauri kan zirga-zirgar ababen hawa, jama’a na fargabar cewa za a iya ci gaba da salwantar rayuka.
