Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Musa Adamu wanda harwala yau kwamishinan lafiya a jihar, tsohon ɗan siyasa ne da ya riƙe mukamai daban daban a gwamnatocin da suka gabata.
Yayi ɗan majalisar dokokin jihar Katsina lokacin marigayi Umaru Musa Yar’adua na gwamnan Katsina.
Haka kuma ya riƙe muƙamin kwamishinan a ma’aikatu daban daban a gwamnatin Ibrahim Shehu Shema.
Ana masa kallon ƙwarewar sa da yadda yake mu’amala da al’ummar yankin sa da jihar baki ɗaya zai taka rawa gaya wajan cimma muradun gwamnatin Bola Tinubu da Dikko Raɗɗa.
Kwamred Mannir Suleiman shugaban Gidauniyar Gwagware Musa Adamu ya bayyana cewa muƙamin da Musa Adamu ya samu an saka ƙwarya a gurbin ta.
” Hon Musa Adamu Funtua shugaban al’umma ne da ya daɗe yana kyautatawa yankin sa da jihar baki ɗaya wanda hakan yasa ya taka rawar gani a siyasar jihar tun lokacin mulkin marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua,”inji Kwamred Suleiman.
“Musa Adamu na gidan kowa a yankin Funtua da wasu sassan jihar,”inji Mannir Suleiman.
Yayi fatan al’ummar jihar Katsina za su ba kwamishinan goyon baya wajen kawowa jihar Katsina abubuwan cigaba ta hanyar wannan muƙami da ya samu.
