Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Shugaban Hukumar Tara Kuɗin Shiga na cikin gida wato Nasarawa State Internal Revenue Services, Ahmed Muhammad, ya bayyana cewa hukumar a ‘yan kwanakin baya ta taro kuɗaɗen shiga da sun kai kimanin Naira biliyan 40 sakamakon ƙirƙiro da sabon tsarin tattaro kuɗaɗen shiga da ta yi kwanakin baya wato na yin amfani da mashinan zamani don samun sauƙin karɓan kuɗaɗen haraji a jihar.
Ahmed Muhammed ya sanar da haka ne a lokacin da yake zanta da wakilin mu dangane da harkokin hukumar a ofishin sa dake Lafiya babbar birnin jihar ranar Litinin 23 ga watan Mayun 2022 da ake ciki.
Ya ce jim kaɗan da naɗa shi a matsahin shugaban hukumar sai ya fara gudanar tare da ƙirƙiro da wasu muhimman tsare-tsare na musamman duk da wasu ƙalubale da hukumar ke fuskanta a fannin ababen hawa da rashin isassun ma’aikata da yanayin aiki da sauransu.
Ya cigaba da bayyana cewa, “ka ga ba yabon kai ko wani abu makamancin haka ba. Kawo yanzu mun tattaro kimanin Naira biliyan 40 da kuma wasu ƙarin biliyan 8 zuwa 10 da a yanzu muke karɓowa a matsayin haraji da sauran su.
“Kuma mun samu ƙari a kuɗaɗen da muke samu a kowane wata guda wato daga Naira miliyan 500 wato a lokacin da aka naɗa ni kenan zuwa biliyan ɗaya da rabi a cikin watan Satumbar shekara da ta wuce ta 2021. Kuma mun samu waɗannan ƙari ko in ce cigaba ne sakamakon waɗannan sabbin tsare-tsare da muka ƙirƙiro kuma muke aiwatarwa a yanzu,” inji shi.
Daga nan sai shugaban hukumar tara kuɗin shigar na jihar ya yi amfani da damar inda ya yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da tallafi da gudunmawa da yake bai wa hukumar don tabbatar da nasarar sabbin tsare-tsaren, inda ya buƙaci kamfanoni da ƙungiyoyi da sauran cibiyoyi da al’ummar jihar baki ɗaya su cigaba da bai wa hukumar cikakken goyon baya don tabbatar da ɗorewar nasarorin.
