Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
‘Yan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna sun yi barazanar hana amfanin da titin Kaduna zuwa Abuja gabaɗaya idan Gwamnatin Tarayya ba ta saki yan’uwansu ba.
Shugaban ‘yan ta’addan, Abu Barrah, ya bayyana hakan ne ga Tukur Mamu, shugaban kamfanin jaridar Desert Herald.
Abu Barrah ya qara da cewa saboda su Gwamnatin Tarayya ta ɗage ranar dawo da amfani da jirgin ƙasan. Ya ce: “Za mu saki sauran fasinjojin idan aka saki wasu kwamandojinmu dake hannun gwamnati.
“Idan gwamnati ta ƙi amsa buqatunmu. Muna gargaɗin ‘yan Nijeriya musamman masu hawa jirgin ƙasa da bin titin Abuja su daina saboda za mu fara kai hari ba ƙaƙƙautawa, kuma babu wanda ya isa ya hanamu.”
Shugaban ‘yan ta’addan ya qara da cewa ba su buƙatan kuɗi. Kuma za su ga cewa waɗanda ke hannunsu na cikin ƙoshin lafiya.
Ya ce: “Ba mu buƙatar kuɗi. Muna da dalilin yin abinda muka yi, kuma idan ba a biya buƙatunmu ba, babu fasinja da zai fito da rai ko da za mu mutu tare ne.”
Ya ce sun aike wa Tukur Mamu saƙonsu ne saboda suna ganinsa tare da Sheikh Gumi a cikin daji.
