Bayan naɗa sabon Akanta-Janar Anamekwe, an gano EFCC na bincikensa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sabon Akanta-Janar na riƙon ƙwarya a Nijeriya yana cikin tuhume-tuhumen Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC)

Ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamnatin Tarayya ta naɗa Anamekwe Nwabuoku a matsayin Akanta-Janar na Nijeriya na riƙon ƙwarya, bayan samun Ahmed Idris da Hukumar EFCC ta yi da zargin karkatar da kuɗaɗe ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi, wanda ta zarge shi da karkatar da Naira biliyan 80.

To sai dai shi ma sabon da aka naɗa, Anamekwe Nwabuoku, akwai zarge-zarge na cin hanci da rashawa a kansa, inda tuntuni yake ƙarƙashin bincike a hukumar EFCC.

Sai dai kuma wata jarida mai suna Economic Confidential ta bankaɗo cewa ashe Akanta-Janar ɗin na riƙon kwaryar shi ma akwai zarge-zarge na cin hanci a rataye a wuyansa.

Rahoton ya bayyana cewa Nwabuoku ya yi wa kansa da kansa aringizon kuɗaɗe a ma’aikatun da ya riƙe.

Jaridar ta kuma jiyo cewa tuni ma hukumomin yaƙi da cin hanci suka ƙwace wasu daga cikin kadarorin da ya mallaka.

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa laifi mafi girma da ya aikata shi ne yadda ya riƙa satar kuɗaɗen a lokacin ya na Daraktan Kuɗaɗe da Asusu a Ma’aikatar Tsaron Ƙasa, inda aka ce ya azurta kansa da kuɗaɗen da ake warewa harkar tsaro na cikin gida.

Sannan jaridar ta bankaɗo cewa ya aikata almundahanar kuɗaɗe da dama a ma’aikatu da dama da ya riƙe.

Saura ‘yan watanni ƙalilan Nwabuoku ya kai shekarun yin murabus a aiki.