2023: Sarkin Damaturu, El-Kanemi, ya yi wa Osinbajo fatan nasara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sarkin Damaturu, Hashimi II El-Kanemi, ya ce masarautar za ta goyi bayan mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo tare da yin addu’a akan Allah Ya sa ya zama shugaban ƙasa a 2023.

El-Kanemi ya yi wannan alƙawarin ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin mataimakin shugaban ƙasar wanda ya kai ziyarar ban-girma a fadarsa ranar Litinin a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Osinbajo ya je Yobe ne a cigaba da tuntuɓar sa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC gabanin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.

Basaraken ya ce ziyarar da mataimakin shugaban ƙasar ya kai fadar wata alama ce da ke nuna girmamawar da ya ke da ita ga masarautun gargajiya.

“Abin da muke sa rai shi ne cigaba; don ɗora wa daga inda a ka tsaya, kuma daga nan ne za ku cigaba.

“Muna godiya ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari; idan ka kawo batun tsaro, gwamnanmu zai bada shaida kan abin da ya faru a jihar nan; amma da Buhari ya hau mulki, sai al’amura suka gyaru; abubuwa sun canza, mun samu zaman lafiya.

“Mun shaida zaman lafiya a wannan gwamnati; Shugaba Buhari ya yi aiki sosai a ƙasar nan mai girma; yana yin abubuwa da yawa duk da ƙalubale; muna buƙatar mu yi godiya ga shugabancin ku.

“Da yardar Allah za mu sa ku a cikin addu’o’i da goyon baya ta kowace fuska don ganin kun yi fice; kuma a ƙarshen wannan rana muna addu’ar Allah Ya sa ka zama shugaban wannan ƙasa mai albarka Nijeriya.”

A nashi ɓangaren, mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci El-Kanemi da ya gode wa gwamnan, wanda a cewar sa, ya kasance abokin tarayya, mai goyon baya da kuma amana; da abin da ya yi wa jam’iyyar.

“Amma a yau, na zo ne domin ganawa da wakilan jam’iyyarmu ta APC, waɗanda za su zavi ko za su tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyarmu; ɗan takarar jam’iyyar mu a zaɓe mai zuwa a 2023,” inji shi.