Galadiman Legas ya nemi matasa su zage damtse wajen neman ilimi da koyon sana’o’i

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Galadiman Legas, Alhaji Aliyu Bambado, ya yi kira ga matasan Arewacin Nijeriya da ma na ƙasar baki ɗaya da su ƙara ƙaimi wajen neman ilimin zamani da na addini tare da koyon sana’o’in hannu domin samun damar dogaro da kai da kuma inganta rayuwarsu.

Galadiman ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin wasu gungun matasa daga unguwanni daban-daban na jihohin Legas da Ogun, waɗanda suka kai masa ziyarar gaisuwa tare da taya shi murnar zagayowar Babbar Sallah ta bana lafiya.

Da yake jawabi bayan kammala karɓar baƙuncin nasu, Alhaji Aliyu Bambado ya nuna farin cikinsa da wannan ziyara ta sada zumunci, yana mai cewa irin waɗannan ziyarce-ziyarcen na taimakawa wajen ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakanin al’umma.

Ya jaddada cewa addinin Musulunci ya ƙarfafa gudanar da irin waɗannan ziyarce-ziyarcen, yana mai cewa Manzon Allah (SAW) ya yi bayanai masu yawa kan muhimmancin sada zumunci da kyautata alaƙa tsakanin Musulmi. A cewarsa, duk wanda ya kasance mai kula da zumunci zai amfana da hakan a duniya da kuma lahira.

Galadiman ya kuma yi kira ga matasa da su mayar da hankali wajen neman ilimi, yana mai cewa ilimi shi ne ginshiƙin ci gaba da cigaban kowace al’umma. Ya bayyana cewa jahilci da rashin ilimi na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa wasu matsalolin tsaro da ake fuskanta a wasu sassan Arewacin Nijeriya.

“Ya kamata matasanmu su rungumi ilimi da kuma sana’o’in dogaro da kai domin kauce wa zaman banza da kuma faɗawa cikin munanan halaye da ka iya lalata rayuwarsu,” inji shi.

Da yake tsokaci kan harkokin siyasa, Galadiman ya shawarci matasa da su guji zama kayan aikin ‘yan siyasa ko shiga ƙungiyoyin da ba su da amfani ga rayuwarsu. Ya ce ya kamata su mayar da hankali wajen gina makomarsu da kuma bunƙasa rayuwarsu ta hanyar halal.

Haka kuma, ya yi kira ga ‘yan siyasa musamman masu riƙe da madafun iko da su taka rawar gani wajen samar da damammakin ci gaba ga matasa ta fuskar ilimi, horo da samar da ayyukan yi.

A ƙarshe, Alhaji Aliyu Bambado ya buƙaci sarakunan Hausawa da sauran shugabannin al’ummomin Arewacin Nijeriya da ke zaune a Legas da su ci gaba da jan hankalin mabiyansu zuwa tafarkin gaskiya, zaman lafiya da haɗin kai.

Ya ce akwai buƙatar al’ummomi su haɗa kai su zama tsintsiya madaurinki ɗaya domin kare muradunsu da kuma yin magana da murya guda idan buƙatar hakan ta taso.

“Haɗin kai, zaman lafiya da fahimtar juna su ne ginshiƙan ci gaban kowace al’umma. Don haka ya kamata mu ci gaba da ƙarfafa waɗannan kyawawan ɗabi’u a tsakanin jama’armu,” inji Galadiman Legas.

By ukarofi

Leave a Reply