2023: Yari ya yi kira ga haɗin kai tsakanin mambobin APC a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar ya yi kira ga mambobi da magoya bayan Jam’iyyar APC a jihar da su kasance tsintsiya maɗaurinki ɗaya don samun nasarar jam’iyyar a zaɓen 2023.

Yari ya yi kiran ne yayin da yake tsokaci kan sulhu tsakanin shi da Sanata Kabiru Garba Marafa da Gwamna Bello Matawallen Maradun a zantawa da manema labarai a gidansa.

A cewar shi, kiran ya zama dole bisa la’akari da babban zaɓe da ke gabatowa.

“Babu wani cigaban ƙasa da za a samu a kowace al’umma ko siyasa idan babu haɗin kai a tsakanin al’umma,” Yari ya bayyana.

Ya bayyana sulhu tsakanin shi da Sanata Kabiru Garba Marafa da Gwamna Bello Mohammed Matawalle da cewar ba domin buƙatunsu ba ne daidai don cigaban jihar da kuma Jam’iyyar APC a zaɓen 2023.

Haka zalika game da matsalar tsaro a jihar, Yari ya bayyana cewa za su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin jihar, jami’an tsaro da kuma Gwamnatin Tarayya, domin kawo ƙarshen matsalar da kuma maido da zaman lafiya a faɗin jihar.

“Za mu yi aiki tare da duk masu ruwa da tsaki don tabbatar da zaman lafiya ya dawo a jihar Zamfara da yardar Allah Maƙaukaki,” Yari ya bayyana.

Ya yi kira ga mambobi da kuma magoya bayan APC a jihar da su zama masu bin doka da kuma kauce wa duk wani nau’i na kawo ruɗani da zai iya kawo naƙasu a jam’iyyar APC don samun nasarar da aka sanya a gaba.