Tsoron Allah wajibi ne a sana’armu, inji Dakta Yunusa Wanzam

Daga MOHAMMED ALI a Gombe

Zannan Askan Sarkin Gombe kuma Sarkin Askan Bolari ta cikin garin Gombe, Dakta Yunusa Wanzam, ya yi iƙirarin cewa, duk wanda ba ya tsoron Allah to ba zai taɓa yin tasiri a tsakanin wanzamai ba.

Ikirarin nasa ba ya rasa nasaba da yadda cikin ‘yan kwanakin nan wasu ke fakewa da sunan masana a harkar maganin gargajiya amma kuma sam ba su da ilimi a kan harkar.

A lokacin da yake hira da wakilanmu a harabar warakarsa a Bolari, Gombe, Dr. Yunusa Wanzam, ya ja hankalin irin waɗannan mutane da su ji tsoron Allah, saboda sana’arsu akwai hatsari a ciki idan mutum bai qware ba, ya tsunduma a ciki.

A cewar shi, “ka ga rayukan masu jinya za su shiga matsala kuma idan ba a yi sa’a ba, sai a rasa rai, saboda haka, dole mu ji tsoron Allah a sana’armu, waɗanda ba su da ilimi a kai, to su yi maza su je su sami horo a akai, ba kamar wanda tun asalin gidansu da shi suka taso kamar ire-iren mu.”

Dakta Yunusa wanda kwanan nan wasu jami’an Kungiyar Lafiya ta Duniya wato WHO da kuma Ƙungiyar Tallafawa Ilimin Yara ta Duniya wato UNESCO, suka ziyarce shi a Gombe akan shaharasa, ya yi kira ga al’umma da kada su faskara wajen tuntuvar masana magani gargajiya da zaran sun kamu da rashin lafiya, mai makon su rinƙa neman taimako daga waɗanda ba su san kome a harkar ba.

A cikin garin Abuja, musamman Garki da kasuwannin Wuse da Gwagwalada, mutane da dama da Dakta Yunusa ya warkar, sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tallafa wa irin shi wajen bubbuɗe musu asibitocin warakar Islama da na gargajiya.