Zaɓen fidda gwani: INEC ta sahale wa jam’iyyu ƙarin kwanaki

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta sahale wa jam’iyyun siyasa ƙarin kwanaki shida kan su kammala komai dangane da zaɓuɓɓukansu na fidda da gwani.

INEC ta sahale wa jam’iyyun ranakun 4 zuwa 9 na Yunin 2022 kan su kammala zaɓuɓɓukan fidda gwani tare da miƙa sunayen ‘yan takararsu bayan da jam’iyyun suka roƙi INEC ɗin ƙarin lokaci.

Hukumar zaɓen ta ce, da farko jam’iyyun sun buƙaci ƙarin lokaci amma ta hana saboda ba ta yarda da duk wani abun da zai jirkita mata jadawalinta ba.

Ta ƙara da cewa, bayan da ta fahimci babu wani aiki tsakanin 4 zuwa 9 ga Yuni, kuma ko da ta bai wa jam’iyyun damar yin amfani da kwanakin hakan ba zai sauya mata tsarin jadawali ba, shi ya sa INEC ɗin ta lamunce wa jam’iyyun gudanar da harkokinsu a tsakanin waɗannan kwanakin.

Sanar manema labarai da INEC ta fitar ta hannun Shugaban Sashenta na Yaɗa Labarai, Festus Okoye, ta nuna bayan kammala zaɓuɓɓukan fidda gwani na jam’iyyun, abu na gaba shi ne karɓar sunayen ‘yan takarar da kowace jam’iyya a tsayar ta intanet.