Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe
Wani mazaunin garin Gombe, Malam Usman Siraka, ya bayyana ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar APC, Dakta Jamilu Isiyaku Gwamna, a matsayin “zabin Allah” ga al’ummar jihar, yana mai cewa lokaci ya yi da zai jagoranci jihar domin ci gaba da bunƙasa ta.
Siraka ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci kan harkokin siyasa a jihar, inda ya ce tarihin jajircewa, haƙuri da kuma ƙoƙarin da Dakta Jamilu ya yi tsawon shekaru wajen neman shugabancin jihar ya nuna cewa mutum ne mai hangen nesa da ƙudurin yi wa jama’a hidima.
A cewarsa, Dakta Jamilu Gwamna ya shafe kusan shekaru 20 yana fafutukar neman zama gwamnan Jihar Gombe, duk da ƙalubale da dama da ya fuskanta a wannan tafiya ta siyasa.
“Mutane da dama sun shaida irin haƙurin da Jamilu Gwamna ya yi tsawon shekaru. Duk da cewa bai samu nasara a wasu lokuta ba, bai daina fafutuka da yi wa jama’a hidima ba. Wannan ya nuna jajircewarsa da kuma ƙaunar da yake yi wa al’ummar Gombe,” in ji Usman Siraka.
Ya ƙara da cewa akwai karin maganar Hausawa da ke cewa ‘zabin Allah shi ne zabi mafi alheri’, yana mai bayyana cewa lokacin da Dakta Jamilu ya samu tikitin takarar gwamna wata alama ce da ke nuna cewa Allah ne Ya zaɓe shi domin ya jagoranci jihar.
Malam Usman Siraka ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Gombe da su ajiye bambance-bambancen siyasa, ƙabila da mazhaba, su haɗa kai wajen marawa ɗan takarar baya domin samun ci gaba da bunƙasar jihar.
“Gombe ta fi kowane mutum muhimmanci. Don haka ya kamata mu haɗa kai domin tallafa wa wanda muke ganin zai kawo ci gaba ga jihar. Lokaci ne na haɗin kai da neman ci gaban al’umma,” inji shi.
Siraka ya kuma yabawa Dakta Jamilu kan rawar da ya taka wajen samar da ayyukan yi ga matasa a lokutan da ya riƙe muƙamai daban-daban na gwamnati da kamfanoni.
Ya ce tun daga lokacin da Dakta Jamilu ya yi aiki a hukumomi da kwamitocin gwamnati har zuwa lokacin da ya kasance cikin shugabannin kamfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO, ya kasance yana taimakawa matasa da dama wajen samun guraben aiki da hanyoyin dogaro da kai.
A cewarsa, idan aka ba shi damar jagorantar Jihar Gombe, zai mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi, inganta tattalin arziki, ƙarfafa matasa da mata, tare da aiwatar da ayyukan raya ƙasa da za su amfanar da al’umma baki ɗaya.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa idan Dakta Jamilu Isiyaku Gwamna ya zama gwamna, Jihar Gombe za ta samu sabon salo na ci gaba da zai sa ta zama abin koyi a tsakanin jihohin Nijeriya.
