•Ta ce za ta cigaba da rushe gine-gine da aka yi ba bisa ƙa’ida ba
Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Hukumar Tsara Manyan Birane na Gwamnatin Jihar Nasarawa, wato Nasarawa State Urban Development Board (NUDB) a turance, ta gargaɗi al’ummar jihar baki ɗaya dangane da mallakar filaye ko yin gine-gine ba bisa ƙa’ida ba a manyan biranen jihar.
Manajan daraktan hukumar, Injiniya Idris Wada ne yayi wannan gargaɗi a lokacin da yake zantawa da wakilin mu a ofishin sa dake babbar hedikwatar hukumar a Lafiya babban birnin jihar ranar Litinin 23 ga watan Mayun shekarar 2022 da ake ciki.
A cewarsa yawancin rushe-rushe da hukumar ke yi musamman a manyan biranen jihar da suka haɗa da Karu da Keffi da Akwanga da Doma da Lafiya da sauran su tana yi ne sakamakon rashin bin ƙa’idojin gine-gine da mallakar filaye a jihar da wasu ke yi wanda a ƙarshe sai hakan ya riƙa haifar da cunkoso da ambaliyar ruwa, rugujewar gine-ginen da sauransu.
Ya ce maimakon haka ya kamata duk waɗanda ke son mallakar filayen ko gine-gine a manyan biranen jihar kafin su yi haka su tabbatar sun tuntuɓi hedikwatar hukumar dake Lafiya ko ofishohin su na shiyya dake duka manyan biranen jihar don samun dama da bayyanai akan ƙa’idojin fara aikin.
Injiniya Yahawa Wada ya kuma yi amfani da damar inda ya bayyana wasu daga cikin ƙa’idojin mallakar filaye ko gine-gine a manyan biranen cewa sun haɗa da samun takardar mallakar fili wato wanda aka fi sani da C OF R ko R of C a turance da gayyayar ƙwararru daga hukumar don duba wuraran ginin da tsarin ginin daga ƙwararru dake da rajista da rahoton nazari na musamman akan filin ginin da dai sauransu, inda ya ƙara da cewa sai hukumar ta amince ta kuma bada dama ga duk wanda ke son fara aikin kafin ya fara, bayan ya cika duka sharuɗa ko ƙa’idojin kenan.
Daga nan sai manajan daraktan ya yi amfani da damar inda ya jaddada cewa hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba a ƙoƙari da take yi na tabbatar ta sake tsara manyan biranen jihar yadda ya dace daidai da zamani, inda ya gargaɗi maniyyata sayin filaye ko fara gine-gine a manyan biranen jihar su tabbatar suna bin ƙa’idojin don kaurace wa fushin hukumar. Ya kuma yi amfani da damar inda ya yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da namijin ƙoƙari da yake yi a fannin sake tsara jihar inda ya ce inda ya ƙara da cewa ba shakka kawo yanzu birane da sauran garuruwan jihar baki ɗaya sun samu sabon fatsali kuma al’ummar jihar baki ɗaya suna yaba tare da yin alfa’ari da haka a kullum.
Idan ba a manta ba a ‘yan kwanakin baya ne hukumar ta aiwatar da wani shirin ta nu musamman na rushe duka gine-gine da ake yi ba bisa ƙa’ida ba a manyan garuruwa ko biranen ta daka faɗin jihar baki ɗaya.
