Kuskure ne saka sarakuna a tsarin mulkin Nijeriya, inji Sarkin Dutse

Spread the love

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji (Dr.) Nuhu Muhammad Sunusi, ya ce kuskure ne sama wa sarakuna matsayi a cikin tsarin dokokin ƙasa kamar yadda majalisar ƙasa ta yi yunƙurin yi kwanan baya.

Sarkin ya ce ya ji daɗin yadda ƙudirin ya faɗi bai kai ga samun nasara ba a Zaure Majalisar Nijeriya a lokacin da aka tafka mahawa akan lamarin.

Sakin ya faɗi haka ne a lokacin da ya amshi baƙuncin shugaban majalisar dokoki ta Nijeriya Sanata Ahmed Lawan a fadarsa da ya kawo masa ziyarar bangirma tare da neman goyan bayansa akan buƙatarsa ta neman takarar kujerar shugabancin Nijeriya.

Sarkin ya ƙara da cewar sarakuna ba sa neman a sakasu a cikin tsarin mulki ko bada shawara ga gwamnati su, sarakuna ba sa buƙatar duk wani matsayi a gwamnati domin hakan na zama wani tarnaki a wajensu da zai hanasu gudanar da aikinsu na masarautu kamar yadda suka saba, a cewarsa.

Ya ce su sarakuna iyaye ne kuma ba sa son katsalandan a cikin aikinsu na fada, amma saboda siyasa ya sa wasu jami’an gwamnati da wasu manyan ‘yan siyasa suke yi wa sarakuna katsalandan a cikin harkokinsu na mulki, idan sun ɗauki matakin ladabtarwa akan wani da ya yi laifi sai a ɓullo ta bayan gida a ciwa basaraken da ya yi hukuncin mutunci a zubar masa da mutunci, inji sarkin.

Ya buƙaci ‘yan siyasa su daina shiga cikin harkokin sarakuna suna yi masu kutse, inda ya ce yanzu ta kai yadda ɗan sintiri yake da daraja ba a ganin mai unguwa da waccan darajar saboda siyasa ta shiga cikin harkokin fada ta lalata komai.

Mai martaba ya ƙara da cewa, “da an bar sarakuna suna yin aikinsu kamar yadda a baya ba a yi masu katsalandan, da ba a samu taɓarɓarewar rashin tsaro ba a Nijeriya, saboda haka sarakuna ba sa neman wani matsayi a kundin tsarin mulkin Nijeriya domin mu iyaye ne.”

Ya ci gabada cewar su abinda suke buƙata daga wajen gwamnati shine Gwamnatin Tarayya ta bar jihohi su bai wa sarakuna damar tafiyar da da harkokinsu kamar yadda gwamnatin jihar Jigawa ta bai wa sarakunan dama da a ce sauran sarakuna sun sami irin wannan damar da ba a sami matsalolin Boko Haram, satar mutane da fashi da makami da sauran ayyukan ashsha ba da suka yi katutu a wasu sassan Nijeriya ba.

Mai martaba Dr. Nuhu Muhammad Sunusi ya kuma yi wa Sanata Ahmad Lawan fatan alheri da kuma fatan Allah ya ba shi shugabancin Nijeriya.

Ya kuma yi kira a gare shi da idan ya zama Shugaban Ƙasa ya yi ƙoƙari dawo da wancan ƙudiri don yi masa gyaran fuska ya zama doka don kawo gyara a masarautun gargajiya

Sarkin ya kuma nuna duwarsa matuƙa gaya akan yadda aka yi watsi da sarakunan ba a kula da su, inda ya ce har yanzu a wasu masarautun masu unguwa ba su da albashin kirki, a cewarsa hakan ya taimaka wajen rugujewar darajar masarautu a wasu sassan ƙasar nan.

Da yake nasa jawabin, mai neman takarar shugaban ƙasar, Sanata Ahmad Lawan, ya ce ya san wasu daga cikin matsalolin Nijeriya, saboda haka ne ma yake tunanin idan ya samu shugaban ƙasa abu ne mai sauƙi da zai yi wajen magance matsalar rashin tsaro a Nijeriya.

Ya kuma ci alwashin inganta ilimi da aikin gona da samar wa matasa aikin yi.

Ya ce ya lura sosai rashin aikin yi da zaman banza shine yake sa matasa suke shiga harkokin fashi da garkuwa da mutane da garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci.

Ya ƙara da cewar samar wa matasa aikin yi da ba su ilimi ita ce hanya ɗaya tilo da za ta yi maganin matsalar rashin tsaro a faɗin Nijeriya matuƙar matasa suna da ilimi da aikin yi babu wanda zai je ya shiga ayyukan ta’addanci.

By Editor