Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamna Aminu Masari ya bayyana cewa al’ummar Jihar Katsina sun ga bala’in ‘yan bindiga, a cikin mummunan tashin hankalin da aka shiga matsananciyar wahala.
Masari ya ce bala’i ya yi tsananin da an fatattaki mutane daga yankunansu, har ta kai sama da Katsinawa 13,000 sun yi gudun hijira zuwa cikin Jamhuriyar Nijar.
Katsina na daga cikin jihohin Arewa maso Gabas da ‘yan bindiga suka hana zaman lafiya.
Masari na magana ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi, wanda ya je a matsayin sa na ɗaya daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC.
Fayemi ya je Katsina a ranar Lahadi, domin ganawa da wakilan zaɓen ‘yan takarar shugaban ƙasa na jihar Katsina, domin ya nemi goyon bayan su.
Ya ce ‘yan Jihar Katsina, musamman Waɗanda suka yi iyaka ko maƙautaka da Dajin Rugu ne suka fi ɗanɗana bala’in ‘yan bindiga.
“Maigirma Gwamna, ka yi maganar yadda matsalar tsaro ta kassara jihar Katsina. To Ina sanar da kai cewa farfaɗo da tattalin arziki a yankin da matsalar tsaro ta yi wa illa ya na da muhimmanci sosai. Wasu mutanen sun yi gudun hijira, wasu sun rasa komai sun danna cikin garuruwan da danginsu suke suna zama da rayuwar takaici.
“Kai ko a yanzu suka koma yankunan su, to babu wani abin dogara domin su rayu da su ke da shi. Saboda an sace masu dabbobi.
“A yanzu haka akwai ƙauyen da ake kira Shimfiɗa a cikin Ƙaramar Hukumar Jibiya. Bayan da ‘yan bindiga suka kori mutanen garin. Sun banka wa garin wuta. Yanzu haka muna kashe Naira miliyan 100 domin sake farfaɗo da garin Shimfiɗa,” inji Masari.
