Sin ba ta da buƙatar adana abinci daga kasuwar ƙasa da ƙasa

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Game da kalaman da wasu ƙasashen yamma suka yi wai ƙasar Sin tana adana abinci daga kasuwar ƙasa da ƙasa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labarai cewa, ƙasar Sin tana da sharaɗi da ƙarfi da kuma imani wajen samar da isasshen abinci ga al’ummun ƙasarta, kuma babu buƙatar ta adana hatsi daga kasuwar ƙasa da ƙasa.

Wang Wenbin ya ƙara da cewa, tun bayan ɓarkewar annobar cutar COVID-19, ƙasar Sin ta samar wa wasu ƙasashe tallafin abinci cikin gaggawa bisa shawarar MƊD da sauran ƙungiyoyin kasa da kasa, don haka ƙasashen duniya sun yabawa ƙoƙarin da ƙasar Sin take domin samar da abinci ga al’ummun ƙasashen duniya, kana ƙasar Sin ita ma ta yi kira ga ƙasa da ƙasa cewa, bai kamata su ɓarnata abinci ba.

A sa’i ɗaya kuma Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, “Muna baƙin cikin ganin yadda wasu ƙasashe masu tasowa suke fama da ƙarancin abinci, amma wasu ƙasashe masu ci gaba suke zubar da abincin. Alƙaluman da ma’aikatar aikin gona ta ƙasar Amurka ta fitar sun nuna cewa, a kowace shekara adadin abincin da Amurka ke ɓatawa ya kai kaso 30 zuwa 40 bisa ɗari na daukacin abincin da ake samarwa al’ummun ƙasar, inda adadin ya kai tan miliyan 103 a shekarar 2018, wanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 161.

Don haka, muna fatan wasu kasashen da abin ya shafa, za su rage abincin da suke batawa, haka kuma su sauke nauyin dake bisa wuyansu, ta yadda za a tabbatar da daidaiton cinikin kayayyakin aikin gona a kasuwar ƙasa da ƙasa, tare kuma da samar da isasshen abinci ga dukkanin al’ummomin ƙasa da kasa.”

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa

By Editor