Daga CMG HAUSA
Yau Juma’a kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin ya yi tsokaci yayin taron ganawa da manema labaran da aka shirya cewa, a matsayinta na ƙasar dake shugabancin BRICS a bana, ƙasar Sin tana goyon bayan ƙasashen ƙungiyar, da su ƙara haɓaka mambobinsu, tare kuma da ƙarfafa haɗin gwiwar dake tsakaninsu da sauran ƙasashen duniya, tana kuma fatan ƙarin ƙasashe waɗanda ke da muradu iri ɗaya za su shiga kungiyar ta BRICS.
A farkon bana, wasu ƙasashe kamar Argentina sun nuna fatansu na shiga BRICS, Wang Wenbin ya bayyana cewa, ƙungiyar BRICS, muhimmin tsarin gudanar da haɗin gwiwa ne tsakanin ƙasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki, haka kuma babban dandali ne na hadin gwiwar ƙasashe masu tasowa.
Tun bayan da aka kafa ƙungiyar shekaru 16 da suka gabata, ta samu ci gaba yadda ya kamata, kuma hadin gwiwar dake tsakanin ƙasashe mambobin kungiyar a fannoni daban daban yana ƙara ƙarfafa, ana iya cewa, tun farkon kafuwarsa, tsarin haɗin gwiwar dake tsakanin kasashe mambobin ƙungiyar BRICS yana taka babbar rawa kan bunkasuwar ƙasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki da kuma kasashe masu tasowa.
Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa
