
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa’i da Hukumar Yaƙi da Laifukan Rashawa (ICPC) ta yi ya janyo sabon fargaba a harkar siyasa, inda hukumar ta musanta ikirarin cewa El-Rufa’i na fama da cutar haɓo a hannunta.
Tun a ranar 18 ga watan Fabrairu ne tsohon gwamnan yake hannun ICPC bayan Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta sako shi inda ya yi kwana biyu.
Cece-kucen ya samo asali ne a lokacin da Kakakin El-Rufa’in, Muyiwa Adekeye ya yi zargin cewa tsohon gwamnan ya fuskanci matsalar haɓo cikin dare a hannun ICPC.
Haka kuma, ya ce ba a gabatar wa lauyoyinsa takardar izinin tsare tsohon gwamnan na tsawon sama kwana biyu ba.
A cewarsa, iyalan El-Rufa’i da lauyoyinsa suna fuskantar ƙalubale wajen ganawa da shi kai-tsaye.
Tuni dai ICPC ta ƙaryata ikirarin a wata sanarwa inda ta ce batun cewa ya yi fama da haɓo ba gaskiya ba ne, kamar yadda Kakakinta, Okor Odey ya bayyana.
ICPC ta ce lallai El-Rufa’i bai fuskanci kowane irin ƙalubalen rashin lafiya ba a hannunta.
A wani labarin, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta sakin tsohon gwamnan da beli idan ba za ta iya tabbatar da lafiyar da tsaronsa ba.
Da yake martani ta shafukansa na sada zumunta, Atiku ya bayyana cewa lafiyar da jin daɗin El-Rufa’i na da matuƙar muhimmanci ga iyalansa da magoya bayansa.
Ya ce, idan hukumomi ba za su iya tabbatar da lafiyarsa da hakkokinsa na asali ba, abin da ya dace shi ne a ba shi beli ba tare da ɓata lokaci ba.
“Atiku ya ce idan wani abu ya sami El-Rufai, gwamnati za ta ɗauki cikakken alhaki,” inji sanarwar.
Har ila yau, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta fito fili ta bayyana wace hukuma ce ke tsare da shi — ko EFCC ce, ko ICPC, ko DSS — yana mai cewa sirri a irin wannan lamari yana ƙara haifar da shakku a tsakanin jama’a.
Ya kuma yi gargaɗin cewa yaƙi da cin hanci da rashawa bai kamata ya zama makamin siyasa ba, yana mai cewa dole ne a gudanar da adalci ba tare da nuna son kai ko wariya ba.
Ya ƙara da cewa, doka dole ta yi aiki ga kowa da kowa ba tare da tsoro ko son zuciya ba, domin tabbatar da gaskiya da amincewar al’umma da tsarin dimukraɗiyya a hukumance.
