INEC ta fitar da sabon jaddawalin zaɓen 2027, za a yi na shugaban ƙasa a 16 ga Junairu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta fitar da sabon jaddawalin tsare-tsaren babban zaɓen 2027, inda ta sauya lokutan gudanar na shugaban ƙasa da gwamnoni kamar yadda hukuncin dokar zaɓe ta 2026 ya tanada.

INEC ta sanar da cewa, a yanzu za a yi na shugaban ƙasa da ‘yan majalisar dokokin ƙasa a ranar Asabar, 16 ga watan Junairu, 2027, yayin na gwamnoni da ‘yan majalisun dokokin jihohi za su gudana a 6 ga Fabrairu, 2027.

Hakan na zuwa ne bayan kwaskwarima ga Dokar Zaɓe ta 2022 da gabatar da sababbin tsare-tsaren lokuta a ƙarƙashin ta 2026, waɗanda za su bayar da damar yin wasu gyare-gyare gabanin zaɓe da harkokin zaɓe.

Da fari, INEC ta ayyana 20 ga Fabrairu, 2027 a matsayin lokacin gudanar da na shugaban ƙasa da ‘yan majalisar dokokin ƙasa, sai kuma 6 ga Maris na wanda za a yi na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi, kana daga bisani aka samu sauyin.

A sabon jaddawalin, jam’iyyun siyasa za su fara gudanar da zaɓukan fidda gwani ne a ranar 23 ga Afrilu, 2026, sannan a ƙarkare a 30 ga Mayu, 2026, kamar yadda dokar ta hukunta.

Yawon yaƙin neman zaɓe na shugaban ƙasa da ‘yan majalisar dokokin ƙasa zai fara ne daga 19 ga Agustan 2026, yayin da na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi kuma daga 9 ga Satumba, 2026. Kamar yadda dokar ta tanada, za a kammala hakan ne ana sauran kwana ɗaya zaɓe.

Hukumar ta kuma karayi jam’iyyun da su tabbatar da kiyaye sababbin tsare-tsaren, tana mai gargaɗin yin amfani da hukuncin doka akan dukkan wanda aka samu da saɓa musu.

By Babaji