INEC ta garzaya kotu kan sake fasalin na’urar BVAS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ce za ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ba ta damar sake fasalin tsarin tantance masu kaɗa ƙuri’a (BVAS) a gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da za a yi ranar 11 ga Maris, 2023.

Wani babban jami’in hukumar da bai so a ambaci sunansa ya shaida wa Aminiya irin ci gaban da aka samu a ƙarshen mako a Abuja.

Majiyar ta yi nuni da cewa wannan umarni na da matuƙar muhimmanci biyo bayan umarnin da aka ba shi na hana bayanan da ke cikin na’urorin BVAS ɗin har sai an gudanar da bincike tare da bayar da ingantaccen kwafen takardun.

Majiyar wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ta ce INEC za ta buƙaci isasshen lokaci don sake fasalin BVAS da ake buƙata domin gudanar da zaɓen da za a gudanar a dukkan jihohin ƙasar nan 36, ban da babban birnin tarayya Abuja.

Majiyar ta ci gaba da cewa, “A gaskiya ma’aikatar shari’a ta hukumar tana shirin shigar da qara a kotu ranar Litinin domin neman izininta ta sake fasalin BVAS ɗin nata a zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar jiha na ranar Asabar,” inji majiyar.

Majiyar ta bayyana cewa, la’akari da adadin BVAS da ake buqata domin gudanar da zaven a faɗin jihohi, INEC na buƙatar sake fasalin BVAS da aka yi amfani da su a zaven da aka yi a ranar 25 ga watan Maris da tura su rumfunan zave domin gudanar da zaɓen ranar Asabar.

Majiyar ta ƙara da cewa sai da aka tura tawagar ƙwararru ta INEC akan lokaci domin fara gyaran na’urorin, wanda sai an yi ɗaya bayan ɗaya.

Majiyar ta ce wannan umarni na da muhimmanci idan har za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihar a ranar Asabar kamar yadda aka tsara, idan ba haka ba babu makawa sai an ɗage zaɓen.

Ku tuna cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja a ranar Juma’a ta ba ‘yan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour, Peter Obi da takwaransa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar izinin samun damar yin amfani da duk wasu muhimman kayayyakin da INEC ke amfani da su wajen gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga Fabrairu.

Wani kwamitin Kotun Ɗaukaka Ƙara da Mai Shari’a Joseph Ikyegh ya jagoranta ne ya bada umarnin bayan sauraron ƙararraki guda biyu na wasu ‘yan takarar shugaban ƙasa guda biyu da suka shigar da ƙara tare da jam’iyyunsu na siyasa.

Musamman masu neman takarar sun buƙaci kotun da ta tilasta wa INEC da ta ba su damar samun takardun da ta yi amfani da su wajen zaɓen shugaban ƙasa don taimaka musu kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

“Izinin gudanar da binciken ƙwaƙwaf na na’urorin BVAS da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaɓen ofishin shugaban ƙasa a ranar 25 ga Fabrairu.”

Masu shigar da ƙara sun kuma nemi umarnin hana INEC “damuwa da bayanan da ke cikin na’urorin BVAS har sai an gudanar da bincike tare da fitar da Certified True Copy na su”.

Kotun, a nata nazari, ta umurci INEC da ta bai wa masu neman izinin duba dukkan kayan zaɓen da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.

Kotun ta ba masu ƙara damar yin leƙen asiri ta hanyar yanar gizo ko yin kwafin rajistar masu jefa ƙuri’a da katunan zaɓe da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.

“An bada wannan izinin ne ga masu neman izinin gudanar da binciken ƙwaƙwaf na na’urorin BVAS da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaɓen ofishin shugaban Tarayyar Nijeriya na ranar 25 ga Fabrairu, 2023,” inji kotun.