BIDIYO: Atiku da wasu jiga-jigan PDP sun jagoranci zanga-zanga zuwa ofishin INEC

Daga BASHIR ISAH

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, tare da abokin takarsa, Ifeanyi Okowa sun jagoranci zanga-zangar lumana zuwa babban ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a Abuja.

Daga cikin waɗanda aka hango su a dandazon masu zanga-zangar, har da shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, Abiye Sekibo, Dino Melaye da kuma Uche Secondus.

Zanga-zangar ɓangare ne na ci gaba da nuna rashin yarda da sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya da ya guda asabar ta makon jiya, inda mambobin jam’iyyar suke zargin ba a yi adalci ba.

Zanga-zangar wadda aka faro ta daga Legacy House a yankin Maitama a Abuja da misalin ƙarfe 10 na safiyar Litinin, an buƙaci mahalarta kowa ya sanya baƙaƙen kaya yayin zanga-zangar.

Sauran jiga-jigan PDP da aka gayyata zuwa wajen zanga-zangar sun haɗa Shugaban Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na PDP kuma Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanue da Darakta Janar na PCC kuma Gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal da sauransu.

Kalli bidiyon ɓangare na zanga-zangar: