



Daga BELLO A. BABAJI
Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya ziyarci Maiduguri inda ya jajenta wa gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum da Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Garbai bisa ambaliyar da aka yi a birnin wadda ta ɗaiɗaita dubunnan mutane.
Wata takarda da Daraktan Labarai na CDS, Burgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, ta ce Babban Hafsan Tsaron ya taya gwamnatin jihar da al’ummarta jimamin aukuwar ambaliyar, ya na mai cewa abu ne da ba a yi tsammanin sa ba wanda ke da wahalar dakatarwa.
Ya kuma yi fatan kar irin hakan ya sake faruwa tare da tabbatar wa gwamnatin jihar cewa jami’an sojoji za su cigaba da taimaka mata don ganin an magance matsalolin da ka iya haddasa irin haka a nan gaba.
A lokacin da ya ke jawabi, gwamna Zulum ya yaba wa rundunar sojin ƙarƙashin jagorancin Janar Musa musamman kan zuwa da kansa tare da ƴan tawagarsa.
Ya jinjina wa jami’ansu a ƙoƙarinsu na ceto mutanen da lamarin ya rutsa da su.
Sannan, a Fadar Shehun Borno, Janar Musa ya jajenta game da waɗanda suka rasa rayukansu da waɗanda suka rasa kadarorinsu inda ya yi godiya ga Sarkin kasancewarsa uba ga al’umma.
A nasa jawabin, Shehun Borno ya yi godiya ga sojojin kan soyayyar da suka nuna wa jihar da al’ummarta ganin yadda Janar Musa da ƴan tawagarsa suka samar da tallafi ga waɗanda lamarin ya shafa.
