Daga JOHN D. WADA a Lafia
Babbar jami’ar nan mai zaman kanta da ake kira Bingham University da ke Auta-balaifi a ƙaramar hukumar Karu jihar Nasarawa ta gudanar da taron cikar ta shekaru 20 da kafuwa tare da babban bikin yaye wasu ɗaliban ta waɗanda suka kammala karatun digiri din su da waɗanda suka kammala na gaba da digiri da PhD da sauran su karo na shida wato convocation ceremony kenan a turance.
An gudanar da bikin ne a ranar Asabar na mako da ya gabata a cikin babban ɗakin taro na jami’ar da ake kira University Chapel kuma an samu halartar manyan baƙi da masu hannu da shuni daga ciki da wajen jihar ta Nasarawa baki ɗaya.
A yayin bikin wakilin mu ya ruwaito cewa an kuma bai wa ɗaliban da suka kammala karatun nasu na digiri na farko da na digiri na biyu da sauran su da suka yi zara, wato waɗanda suka fi nuna ƙwazo wasu kyaututtuka na musamman daban daban don ƙarfafa su tare da girmama su ta wannann ƙoƙari da bajinta da suka nuna.
A jawabin shugaban jami’ar, Farfesa Haruna Kuje Ayuba ya bayyana cewa jami’ar ta samu ci gaba da dama a duka matakai a shekaru 20 da suka gabata kuma ta sami tallafin kuɗi da wasu tallafin daban daban da dama ciki har da wanda wannan sanannen cibiyar nan ta Bill & Melinda Gates Foundation ta bayar da sauran su.
Ya kuma bayyana cewa jami’ar ta sami takardun shaida na manyan shirye-shirye da dama da hakan ke tabbatar da ita a matsayin cikakkiyar jami’a dake zaman kanta na dindindin cikin waɗannan shekaru 20 zuwa yanzu. Ya kuma taya duka ɗaliban da suka kammala karatun murna tare da jan hankalin su da su kasance jakadun jami’ar nagari a duk inda suka sami kansu nan gaba.
Wasu da suka sami damar jawabi a wajen gagarumin taron mai cike da ɗinbin tarihi duk suma sun yaba wa ƙoƙarin jami’ar ta Bingham musamman ta fannin samar da ingantattun ilimin zamani dana addini wa al’umma baki ɗaya tare da taya ɗaliban murna.
A ƙarshe dai a yayin bikin da aka shirya domin tunawa da shekaru 20 da wanzuwar jami’ar da kuma convocation ɗin karo na 6 an kuma baje kolin wani littafi mai suna “BINGHAM UNIVERSITY @ 20,” a turance wanda ya bayyana cikakkiyar tarihi da tafiyar jami’ar da ta yi a cikin waɗannan shekaru 20 da suka gabata da sauran su.
