Jam’iyya mai mulki ko jam’iyyar gwamnati?

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Idan za a tunawa, Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da ya ke jawabin karɓar takardar lashe zaɓe daga tsohon shugaban hukumar zaɓen Nijeriya Farfesa Attahiru Jega ya zayyana jam’iyyar APC a lokacin da cewa, “jam’iyyar gwamnati ce” ba “jam’iyya mai mulki ba” don yunƙurin nuna APC ba mulki ta zo yi ba amma aiki ta zo yi wa jama’a ta hanyar gwamnati mai inganci.

An yi ta muhawara kan wannan kalamai a lokacin da nuna duk sunayen biyu sammakal ne ko kuma sauya kalmomi ne kawai. Gaskiya ma dai abin da kan bambanta sarauta ko mulkin mulukiyya a madafun iko ga jagoranci shi ne salon yadda a ke tafiyar da amanar al’umma ta nuna adalci ko akasin haka. Ai ’yan siyasa kan zaiyana kowace gwamnatin mulkin soja da ta ’yan kama karya saboda ba jama’a ne su ka zaɓi gwamnatin ba, zai yiwu ma wasu mutnae ne su ka ɗauki bindigogi su ka bi dare su ka kwace mulkin wani lokacin har da zubar da jini. Duk da haka a kan samu gwamnatocin soja da kan tabuka abin kirki ta hanyar yin wasu ayyuka da kan raya ƙasa.

Hakanan a kan samu bin doka ko don dole fiye da yadda ya kan faru a gwamnatocin fararen hula. Ba wai sojoji basa handama ba ne, a’a, amma ba sa bin salo irin na shagali da fararen hula ke yi da nunawa duk wanda ba shi da Naira bai kamata ya amfana da alfarmar ƙasa ba. Kuma a duk lokacin da soja ya yanke wani hukunci za za gaya ɗore don ba wanda zai yi mu su kuma ba wanda ya isa ya kawo wani bambancin yanki ko ƙabila wajen gudanar da lamura.

Hasalima za a a iya ɗaukar mutum daga Oyo a kai shi Borno ya zama kantoman mulkin soja. Fararen hula na da damar yin aiki yadda ya dace ta hanyar bin dokokin tsarin mulki amma ba lalle hakan na faruwa ba. Za ka ji fararen hula na cewa tsarin mulki ko majalisar dokoki na yi mu su tarnaki wajen gudanar da ayyuka. Masu sharhi na cewa ba lalle haka ba ne don in fararen hula za su bi ƙa’idar tsarin mulki kowa ya yi aiki bisa huruminsa, to za a samu mulki mafi inganci da adalci.

Kazalika ko ƙarfin shugaba a Nijeriya daban ne don shugaban farar hula na Nijeriya na da taken mai wuƙa da nama sai kawai ya yanka gefen da ya ke so ya raba kitse da tsoka. A kan samu son kai wajen gudanar da mulkin don za ka ga an ɗauko aiki mai ma’ana amma sai bambancin siyasa ya sa ga wasu sun yi tsalle sun ce ba su yarda ba. Kazalika za ka ga waɗanda ke kan mulki na neman zama sun fi qarfin doka don ko laifi su ka aikata za ka ga ba za a hukunta su ba. In za a tuna tsohon shugaban jam’iyyar gwamnati Adams Oshiomhole ya taɓa cewa da zarar ka dawo jam’iyyar gwamnati tamkar ka tsira daga tuhuma. Ba mamaki ya furta hakan ne don jan hankalin mutane su dawo jam’iyyarsa. Illar kawai yadda jam’iyyar ta hau mulki da kamfen ɗin yin ba sani ba sabo kan ɓarayin biro. Duk ƙasar da kowa ke bin doka da oda ta haƙiƙa za ta samu cigaba.

Hakanan duk wanda ya saba doka ita dokar ta hukunta shi ko wane matsayi ya ke kai to nan ma za a samu shinfiɗar adalci da zaman lafiya. Fararen hula na da damar gyara ƙasa don daga cikin farar hula su ke fitowa su hau kujera bayan gamsar da masu zaɓe cewa za su daidaita lamura. Ko da wani zai ce ba zaɓe a ke yi ba naɗi ne sai ya duba yadda shugaba Buhari ya jajirce da magoya bayan sa har ala tilas a ka ɗauka gaba ɗaya sai BUHARI kuma a ka damƙa ma sa ragama ba tare da ƙalubalantar nasarar sa a gaban kotu ba. Ku tuna shugaba Buhari bai tava faduwa zaɓe bai ƙalubalanci wanda a ka ayyana a matsayin wanda ya samu nasara ba.

Yanzu ga shi a kwana a tashi wannan sabuwar jamhuriya ta cika shekaru 23 cif ba da katsalandan din soja ba kuma har ma ga shi an shiga shekarar zaɓen 2023. Ba ya ga jam’iyyar gwamnati APC da babbar jam’iyyar adawa NNPP, yanzu wasu jam’iyyun ma na tasowa kamar NNPP, Leba ba ya ga irin jam’iyyar APGA ta yankin ƙabilar Igbo da PRP ta NEPU Sawaba.

Masu sharhi na bin bayanan da tarihin siyasar ’yan takarar jam’iyyun don duba yanayin yadaa a ke hasashen zaɓen zai gudana. Zaɓen zai zo ba tare da shugaba Muhammadu Buhari ba don zai kammala wa’adin san a ƙarshe ne a lokacin. Don haka komai zai iya faruwa na nasara ko akasin haka ga kowace jam’iyya komai ƙarfin ta na zahiri da a ke gani wani ƙarfin na baɗini ko bayan fage zai iya ba ta zarra. Dalilin da ya hakan zai faru shi ne kowace jam’iyya ta hau karagar tarayya bisa ma’ana bayan PDP ta yi mulki na tsawon shekaru 16, gungun jam’iyyun adawa sun haɗa kai su ka kafa APC inda su ka lashe zaɓe.

Don haka masu zaɓe sun gane takun kowa da irin yadda gaskiya ko akasin ta ya ke na ’yan siyasar Nijeriya. Wasu kurari ne ko cika baki kawai su ke yi gabanin hawa madafun iko. Wani abun dubawa ma shi ne yadda ’yan siyasa gagga-gagga kan sauya sheƙa daga zuwa jam’iyyar gwamnati da zarar jam’iyyar ta faɗi zaɓe. An ga misalai da dama da ke nuna wasu ’yan siyasa a Nijeriya ba su da wata manufa da ta wuce yadda za su hau karagar mulki ta hanyar kowace hanya kuma ta ko wace jam’iyya kawai tamkar a ce burin maje hajji sallah.

Amfani da ɓangaranci ko ƙabilanci bai dace ya ruɗi masu zaɓe wajen kaɗa ƙuri’arsu ga waɗanda ba su iya komai ba sai ɗaurewa ’yan jari hujja baya su yi ta sukuwa kan dukiyar ƙasa su na yawace-yawace a ƙasashen duniya da halartar bukukuwan shagalin da ba su da wani amfani ga shugabancin da su ke yi.

Magoya bayan manyan ’yan siyasa na fadar dalilan da su ke ganin gwanayen su ne za su lashe babban zaɓen 2023. Muhawarar ta fi ɗaukar hankali a babbar jam’iyyar APC mai mulki da PDP mai adawa.

Yayin da APC ta tsaida tsohon gwamnan Legas Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takara. PDP ta tsaida tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar a matsayin ɗan takara. Dukkan mutanen biyu sanannu ne a fagen siyasar ƙasa kuma sun fara taka rawa tun farkon wannan jamhuriya an dama da su an shanye da su.

A 2007 Atiku ne ɗan takarar shugaban ƙasa na tsohuwar jam’iyyar Tinubu wato ACN wacce ta narke da sauran manyan jam’iyyu ta zama APC ta zamanin yau. Kun ga a wancan lokacin Tinubu na mara baya ga Atiku ya zama shugaban Nijeriya inda hakan bai yiwu ba don Atiku bai lashe zaven ba, shugaba Buhari a lokacin ya na ANPP shi ma bai lashe zaɓen ba, sai marigayi shugaba Umaru Musa ’Yar’adua a PDP ya lashe zaben kuma bai yi kasa a gwiwa ba wajen zayyana zaɓen na sa da cewa ya na da wasu illoli. Hakan ya sa shi kafa kwamitin gyaran lamuran zaɓe na Jostis Muhammad Lawal Uwais.

’Yan APC na cewa Tinubu zai samu ƙuri’un Yarbawa a cure inda zai haɗa da waɗanda zai samu daga gwamnonin APC na Arewa da ke mara ma sa baya. An kuma san gwamnoni da tsananin tasiri a zaɓe ballanta ma a ce ga gwamnonin manyan jihohi irin Kano, Kaduna da Katsina su na marawa ɗan takara baya.

Magoya bayan Atiku na cewa zai samu ɗimbin ƙuri’u daga ’yan arewa da su ka gaji da salon mulkin Buhari inda zai samu na wanda zai tsayar a matsayin mataimaki daga kudu. Hakanan ya yi dace ba a kala ma sa sharrin mai nuna bambancin addini ba ne ko ƙabilanci.

Hakanan wasu na nuna Atiku ya fi Tinubu koshin lafiya don haka masu son sauya shugaba da zai zama kullum ya na kan hanyar asibitocin turai za su zaɓi Atiku.

Duk da haka a na ganin manyan masu ruwa da tsakin siyasa da ke cikin gwamnati za su dage don Tinubu ya samu mulki don su ma hakan ya ba su damar maƙalewa a madafun iko. Haƙiƙa a Nijeriya zai yi wuya mutum ya shiga fadar Aso Rock ya so hakan ya ƙare.

Wani dalilin da a ke ganin zai taimaki Atiku shi ne yankin Arewa maso gabas inda ya fito da bai taba samar da shugaba ba; amma Tinubu na iya samun ta sa nasarar ta hanyar masu ganin ai bayan ɗan arewa ya yi shekaru 8 kan mulki ya dace mulkin ya koma Kudu ba tare da la’akari da kowace jam’iyya ba; don a samu haɗin kan ƙasa da rage kaifin masu rajin kafa Biyafara ko ƙasar Oduduwa.

In an bi ta yawan dangi Atiku zai iya cin gajiyar kasaci ga Hausa Fulani da haƙiƙa sun fi Yarbawa yawa amma zafin marawa ƙabilanci baya ya fi tsanani a tsakanin Yarbawa.

By Editor