Daga CMG HAUSA
A yau Lahadi majalisar gudanarwar ƙasar Sin ta nada manyan jami’an da za su jagoranci gwamnati na 6 na yankin musamman na Hong Kong (HKSAR) na ƙasar, wanda ya yi daidai da amincewar sabon kantoman yankin John Lee, da kuma bisa dacewa da tsarin muhimman dokoki yankin HKSAR.
Lee, wanda ya lashe zaɓen shugabancin yankin, wanda aka gudanar a ranar 8 ga watan Mayun da ya gabata, zai kama aiki daga ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2022 da muke ciki.
Sabbin jami’an da aka zaɓa za su fara aiki ne a rana guda tare da sabon shugaban na yankin HKSAR.
Mai fassarawa: Ahmad
