Jiki da jini (2)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan uwa masu karatu, Assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai ilmintarwa na Jikin Ɗan Adam, wanda ya ke zayyano muku bayanai game da duniyar gangar jikin bil adama, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu, kuma ku san yadda jikinku ya ke aiki, don kula da lafiyarku da rayuwarku ta yadda za ku iya sarrafa shi gwargwadon yadda ya halitta mu.

Kamar yadda na faɗa, shi jiki koyaushe cikin aiki ya ke. Hatta lokacin da muke zaune muna hutawa, da lokacinda muke bacci, kiki baya daina aiki. Sai dai yana rage ƙarfi da yawan ayyukan da yake yi lokacin da muke hutawa da kuma lo kacin da muke bacci.

Duk wani makamashi da muka ƙone lokacin da muke a farke a cikin wuni, yayin gudanar da al’amuranmu na yau da kullum, to lokacin bacci ake samar da sabbin makamashi wanda za mu yi amfani da shi idan Allah ya sa mun wayi gari lafiya. Bayan wannan, sauran sinadarai da mukayi amfani da su cikin wuni suma a lokacinda muke bacci ake samar da sababbi.

Sarkin Halitta Ya tsara jikinmu domin mu gudanar da hidimominmu cikin wuni, sannnan kuma mu huta cikin dare. Yin hakan, ba karamar hikima ce ba.

A cikin litattafanmu na kimiyyar jikin ɗan adam, shi bacci da al’amuran da ke faruwa lokacin baccin, maudu’i ne sukutum guda, mai zaman kansa. Saboda haka zan bar bayanin a nan, idan da hali Allah ya kaimu wani lokacin na samu dama, za ku sha bayani game da yadda jikin ɗan Adam ke aiki lokacin bacci.

Idan kuna so jikinku ya dinga ba ku haɗin kai domin tafiyar da al’amuran yau da kullum, to ya ha da kyau ku dinga hutawa. Ku dinga bacci isasshe, tare da kula da cima, da sauransu. Ina ganin sabin ilimin yadda jikin mutum ke aiki zai taimaka ƙwarai wajen haskawa mutane abubuwan da Kan iya jawowa jiki wanzuwar lafiya, da kuma waɗanda kan iya jawowa jiki rikici da rashin lafiya.

A cigaba da bayanin tsarin yadda jiki ke aiki, Allan ya yi shi ne tamkar wata na’ura lo mashin, ko inji mai sarrafa kansa. Duk lokacin da jikin ɗan adam ya fahimci cewa muhallin da ke kewaye da shi zai iya ta’annati ga zaman lafiyar ƙwayoyin halittun jiki, to haƙiƙa jikin zai ɗauki mataki ba tare da ɓata lokaci ba. Misali: idan ka shiga cikin zafi, jiki zai fara gumi; Iran ka shiga cikin sanyi, jiki zai fara rawar ɗari; Idan kin shaƙi datti ko ƙura ta hancinki, to jiki zai zunguri hanyoyin iska domin a fara tari da atishawa. Waɗannan duk matakai ne na bawa jiki kariya daga abubuwan cutarwa da ke kewaye da mu.

Bugu da ƙari, Iran kaci ko kika ci wani abu da zai iya cutarda jiki, to akwai zaɓi guda biyu: idan wannan abu mai cutarwa yana cikin tumbi ne, to za a yi amai; idan kuma ya wuce tumbi kafin a gano shi, ta za a yi gudawa. Malam, jikin ɗan Adam akwai tsari! Zazzaɓi da kuke gani, ba cuta ba ce, mataki ne da jiki ke ɗauka domin nuni da cewa akwai wata baƙuwar halitta mai cutarwa da ta shiga jiki, saboda haka shi ma zazzaɓi kamar wani nau’i ne na kariya ga jikin ɗan adam.

Allah ya halicci jiki domin ya zamto mai saurin naƙaltar ina aka dosa. Idan kana bacci kullum ƙarfe tara, to fa da zarar tara na dare ta yi, ko a ina kake, jikinka zai fara shirin bacci, sai kawai ka ji ka fara jin bacci. Me yasa haka? Saboda ƙwaƙwalwa ta riga ta taskance ƙa’ida cewa ƙarfe tara na dare, lokacin baccinsa ko lokacin baccinta ne. Duk abin da ka saba yi a wani lokaci ƙayyadde, to wannan lokaci yana yi za ka ji jikinka ya yi shirin gabatar da wannan abu.

Kamar yadda na faɗa, ƙwaƙwalwa nada saurin naƙaltar abin da muke yi yau da kullum. Wannan shi ne dalilin da ya sa; ba ma tunani idan mun yi shirin taka ƙafafunmu domin yin tafiya; ba ma tunanin ya za muyi idan munyi nufin yin magana; ba ma tunanin ta ina za mu fara idan mun yi nufin sanya kaya ko cire su; ba ma tunani idan mun yi nufin shan ruwa ko cin abinci, ko zuwa banɗaki. Duk bayanan yadda ake yin waɗannan abubuwa an taskance su ne a cibiyar haddace bayanai da ke cikin ƙwaƙwalwarka ko ƙwakwalwarki, Wanda a Turance mukafi sani da “memory”.

Shi jikin ɗan Adam bai yadda da ɓarna ba ko almubazzaranci. Sannan kuma yana son tattali. Duk wani aiki da zanyi ko za ka yi ko za ki yi, jiki na duba wacce hanya ce mafi sauri, mafi sauƙi, mafi gamsarwa da za ta sa a gama aikin cikin lokaci taƙaitacce!

Kar ku manta, taken rubutun shi ne “jiki da jini”, wanda Malam Bahaushe ya ce “sai da hutu”. Ina so ku fahimci yadda jikin ɗan Adam ke aiki, kafin kusan yadda za ku yi ku bashi hutun da yake buƙata. Kafin mutum ya yi abu, akwai buƙatar ya san yadda ake yi wannan abu, ko ba haka ba?

Babbar hanyar da za ku bi wajen tabbatar da cewa jikinku ya samu hutun da ake buƙata, ita ce hanyar motsa jiki! Idan kuma kuna tantama da abinda na faɗa, to ku biyo ni sannu domin na warware muku zare-da-abawa.

Wani masani ya ce shi jikin mutum an yi shi ne domin ya yi gumi! Wato sai ana yi ana motsa shi. Idan kana motsa jiki, to shi kansa lokacin da za ka ware domin hutawar sai ya fi maka daɗi. Motsa jiki na nufin “sarrafa motsin jikinka ta yadda fitar numfashinka zai ƙaru; bugun zuciyarka shi ma zai ƙaru; sannan kuma za ka yi gumi.” Da farko shi motsa jiki zai kawo maka ƙaruwar waɗannan abubuwa da na faɗa, amma daga baya mai zai faru? wato bayan ka saba da motsa jikin? Duk abubuwan za su yi ƙasa ne.

A lokacinda baka komai, an ƙiyasta bugun zuciyarka ya zamto sau 72 a duk minti guda. Duk da cewa akwai bambanci tsakanin mutane, shi yasa aka bada ma’auni (tana bugawa sau 60 zuwa 100) a duk minti guda. Idan zuciyarka sai ta harba jini sau 75 a duk minti, to yayin da ka mayar da motsa jiki ɗabi’a, zuciyar za ta iya dawowa harbawa sau 60 ko ƙasa da haka ma. Ta yaya? Saurin bugun da zuciyarka ke yi lokacin da kake tsaka da motsa jikin shi yake ƙara mata qarfi, kuma ya ƙara mata girma, to tun da ta ƙara ƙarfi, ashe ko bata daddage ba, za ta iya harbawa sau 56 a madadin sau 75 da take yi da can. Kaga a nan motsa jiki ya yi rana.

Haka kuma idan a lokacin da ba ka wani abu na aikin ƙarfi, kuma ba ka cikin firgici ko tsoro, za ka dinga numfasawa ne kimanin sau 12 a duk minti ɗaya, ma’aunin shi ne daga sau 12 zuwa sau 16. Shi ma idan kana motsa jiki akai-akai, zai iya dawowa kamar sau 10. Ta yaya? Saboda tsokokinda ke da hurumin taɓewa da shikawa domin su tabbatar da mutum ya numfasa, su na ƙara ƙarfi idan mutum ya na motsa jiki.

Kamar yadda za mu gani, sauran abubuwa da da can sai jiki ya dage sannan zai iya yinsu, rungumar motsa jiki zai sauƙaƙa gabatar da zu waɗannan ayyuka

Masu karatu ku tara a sati mai zuwa domin ci gaba da kawo mu ku bayanai akan jikin ɗan Adam. Kafin nan nake cewa Assalamu alaikum.