Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Fansho ta ƙasa (PenCom) ta bayyana cewa zamanin jinkirin biyan fansho ga ma’aikata masu ritaya ya zama tarihi.
Ibrahim Buwai, shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na PenCom, ya bayyana haka a wata hira da Hukumar Labarai ta Nijeriya (NAN) a Abuja ranar Lahadi.
Buwai ya ce, PenCom ta cimma nasara wajen biyan haƙƙokin fansho cikin lokaci, sakamakon tsauraran gyare-gyare da inganta tsarin aika kuɗi.
Ya ce, tun daga watan Yuli, hukumar na biyan haƙƙoƙin fansho da aka tara kamar yadda ya kamata, domin tabbatar da cewa masu ritaya suna samun haƙƙoƙinsu a cikin watan da suka yi ritaya.
“Har zuwa yau, an kammala biyan fansho ga waɗanda suka yi ritaya a watan Nuwamba. Hakkokin masu ritaya a watan Disamba za a biya kafin ranar 15 kamar yadda aka sanar a baya, domin su samu fa’ida kafin bukukuwan ƙarshen shekara,” inji Buwai.
Ya tuna cewa Gwamnatin Tarayya ta saki biliyan N758 don biyan bashin fansho da ya rage, ciki har da ƙarin fansho da ake bin bashi tun daga shekarar 2007.
Buwai ya ce, waɗannan ci gaban sun nuna jajircewar hukumar wajen tabbatar da cewa babu wani mai ritaya ƙarƙashin Tsarin Fansho (CPS) da zai fuskanci tsaiko ba saboda jinkirin biyan fansho.
“Da waɗannan matakai a wurin, jinkirin biyan fansho ga ma’aikatan MDA da ake biya daga kasafin kuɗi ba zai sake kasancewa matsala ba.
“PenCom na nan a shirye wajen ƙarfafa tsarin fansho da tabbatar da jin daɗin masu ritaya a faɗin ƙasa,” inji shi.
Buwai ya ƙara da cewa, hukumar na aiki tare da masu ruwa da tsaki wajen magance matsalar rashin aika fansho na ma’aikata zuwa Asusun Fansho (PFA) daga hannun ma’aikata.
A kan wannan matsala, Buwai ya ce Daraktar Janar ta PenCom, Ms Omolola Oloworaran, kwanan nan ta rattaba hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci (ICPC) domin dawo da gudummawar fansho da ba a aika ba da tabbatar da bin dokokin fansho.
Ya ce, Yarjejeniyar na bai wa ICPC ikon tilasta biyan kuɗaɗen da aka dawo da su cikin Asusun Ajiya na Ritaya (RSA) da hukunta ma’aikata da suka saɓa doka. Buwai ya ce, duk wanda ya yi gazawa zai fuskanci hukunci bisa ga doka.
