Kaftin ɗin Super Eagles ya ƙara aure

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa kuma Kaftin na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasa Super Eagles, Ahmed Musa, ya ƙara aure.

Musa mai shekaru 29, wannan shi ne aurensa na uku, tun bayan da ya rabu da matarsa ta farko Jamila a 2017 wanda nan take ya maye gurbinta da Juliet kuma suke tare har yanzu.

A halin da ake ciki dai yanzu sabuwar amaryar tasa mai suna Maryam ita ce matarsa ta biyu.

Jarumi a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu, shi ne ya wallafa bayani da hotunan auren a shafinsa na Instagram inda ya taya Ahmad Musa murna.