APC ta tsayar da ranar soma tarurrukanta

Daga AISHA ASAS

Jam’iyyar (APC) ta tsayar da ranar 31 ga Yuli, 2021 a matsayin ranar da za ta soma gudanar da tarurrukanta don zaɓen shugabannin jam’iyya a faɗin ƙasa.

Cikin wata wasiƙa da ta aike wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) mai ɗauke da kwanan wata, 11 Yuli, 2021, APC ta nuna za ta soma tarurrukan nata ne a ranar 31 ga watan Yuni inda za a soma da matakin unguwanni kafin ƙananan hukumomi da jihohi su biyo baya.

Kafin wannan lokaci, APC ta aika wa INEC da wasiƙa a kan ɗage tarurrukan nata da ta shirya gudanarwa da farko gami da babban taronta na ƙasa.

Sai ga shi jam’iyyar ta sake aika wa INEC da wata wasiƙar wadda ta samu sa hannun babban sakatarenta na ƙasa, John James Akpanudoedehe da shugabanta na ƙasa Mai Mala Buni, inda ta sanar da hukumar shirinta na soma gudanar da tarurrukan zaɓen shugabanninta ya zuwa 31 ga Yuli.

A cikin wasiƙar APC ta ce, “…muna sanar da INEC za a fara tarurrukan ne a ranar 31 ga Yulin 2021 wanda za a soma da unguwanni sannan ƙananan hukumomi da jihohi su biyo baya.