Kalaman Xi Jinping game da kishin ƙasa

Daga CMG HAUSA

A bana yau Juma’a ce ranar da Sinawa ke murnar bikin Duanwu. An fara gudanar da wannan biki na musamman ne, domin tunawa da wani shahararren marubucin rubutattun waƙoƙi mai kishin ƙasa mai suna Qu Yuan, wanda ya rayu a zamanin daular Zhanguo wato the Warring States Period a Turance wato tsakanin shekarar 475 zuwa 221 kafin haihuwar Annabi Isa A.S.

Qu, ya rubuta waƙoƙi da dama game da rayuwar al’umma da kishin ƙasa, kuma shugaban ƙasar Sin, babban sakataren kolin JKS, kana shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin ƙasar Xi Jinping, ya kan tsamo wasu kalmomin dake waƙoƙin Qu Yuan, yayin da yake jawabi. Misali ya taba cewa: Ƙaunar ƙasar mu, da daura niyyar bautawa ƙasa, da kewar kasar mu ta haihuwa, nauyi ne dake wuyan dukkanin al’ummar Sinawa.

Tarihin ƙasar Sin ya shafe dubban shekaru, kuma kishin ƙasa ya jima da zama jigo, kuma wani irin ƙarfi dake ingiza dukkanin ƙabilun ƙasar Sin wajen cimma manyan nasarori.

Yayin da ake tunkarar rayuwa ta gaba, dole ne Sinawa su yayata kishin ƙasa, da martaba kimar ƙasa, da samun karfin gwawi tsakanin jama’a, da karfafa manufar “zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya”.