Kamata ya yi ‘yan siyasar Amurka masu cewa suna martaba al’ummar Sinawa su dakatar da kitsa ƙarairayi

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Cikin jawabin sa na baya bayan nan game da manufofin ƙasar Sin, sakataren wajen Amurka Antony Blinken, ya ce Amurka na da manyan bambance bambance tsakanin ta da JKS, da ma gwamnatin ƙasar Sin, amma waɗannan bambance bambance na da nasaba ne da gwamnatocin ƙasashen, da tsarin gudanarwa, ba wai da al’ummun sassan biyu ba.

Sai dai waɗannan kalamai na Mr. Blinken, ba za su samu karɓuwa a kunnuwan Sinawa, da al’ummun ƙasa da ƙasa, da ma shi kan sa Blinken ba. Kasancewar su ƙarya ce tsagwaron ta!

Idan da gaske ne, kamata ya yi ‘yan siyasar Amurka dake cewa suna martaba Sinawa, su rika girmama hanyar ci gaba, da tsarin siyasa da al’ummar Sinawa ta zaba, su kuma girmama JKS, wadda ita ce ke wakiltar ginshikin moriyar ɗaukacin al’ummar Sinawa, sabanin yadda waɗannan ‘yan siyasa ke ƙoƙarin ɓata suna, da tunzura ƙasar Sin.

Yanzu haka dai Amurkawa na fuskantar tarin matsaloli. Kuma ƙalubalolin da ya kamata gwamnatin Amurka ta warware suna da tarin yawa. Cutukan dake damun Amurka ba za su warke, ta hanyar sanya waigi tsakanin JKS da al’ummar ƙasar Sin ba.

Duk irin salon zance da Blinken zai yi amfani da shi a jawabin sa, ba zai iya boye gaskiyar burin Amurka na daƙile ci gaba, da farfadowar ƙasar Sin ba. Daukacin al’ummun Sinawa, da sassan ƙasa da ƙasa na sane da hakan.

Fassarawa: Saminu Alhassan

By Editor