Ba don ni ba da Buhari bai ci zaɓen 2015 ba – Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jagoran Jam’iyyar APC kuma ɗaya daga cikin na kan gaba da ke neman takarar shugabancin Nijeriya a ƙarƙashin jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu ya ce, shi ne ya zama ja gaba a yaqin neman zaɓen Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya yi nasara a 2015.

Tinubu ya ce shi ne ya bayar da sunan Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin abokin takarar Buhari.

Jaridar Dailay Trust ta ruwaito cewa Tinubu ya bayyana hakan ne a masaukin shugaban ƙasa a birnin Abeokuta na jihar Ogun, yayin da yake tattaunawa da daliget ɗin APC gabanin zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar.

Tinubu ya samu rakiyar Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu da takwaransa na Kano Umar Ganduje da kuma tsohon Gwamnan Borno Kasim Shettima.