Sigari na kashe ‘yan Nijeriya 29,000 a kowacce shekara – Bincike

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani mai bincike kan ci gaban tattalin arziki a Afirka ya ce taba sigari na sanadin rayukan ‘yan Nijeriya 29,000 a kowacce shekara.

Austin Iraoya da ke aiki da cibiyar tattalin arziki ta Afirka ya ce ‘yan Nijeriya na kashe Naira biliyan 526 wajen shan sigari da neman maganin cututuka da taba ke haifarwa.

Jaridar Daily Trust a Nijeriya ta rawaito, Mista Austin na cewa wannan al’amari na yin mumunan illa ga tattalin arzikin ƙasa.
Kuma a cewarsa gwamnati na samun harajin kashi 10 cikin 100 ne kacal, na waɗannan kuɗaɗe da ake varnatarwa wajen shan sigari.

Waɗannan bayanai nasa na zuwa ne a lokacin bikin ranar yaƙi da shan taba sigari da aka gudanar a birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja ranar Litinin wannan makon.