Mata zai bar Man United a ƙarshen watan Yuli

Juan Mata zai bar Manchester United a matakin wanda bai da ƙungiyar, idan yarjejeniyarsa ta ƙare a ƙarshen kakar bana.

Mai shekara 34, wanda ya taka rawar da ta kai Sifaniya ta lashe kofin duniya a 2010, ya koma United daga Chelsea a 2014 kan fam miliyan 31.1.

Mata wanda ya ci ƙwallo 51 a wasa 285 da ya yi wa United, ya buga Premier League ta bakwai a kakar nan da aka kammala ranar 22 ga watan watan Mayu.

Ranar Laraba, Manchester United ta sanar da cewar Paul Pogba, wanda kwantiraginsa zai ƙare a bane, zai bar Old Trafford.

Mata, wanda ya tsawaita kwantiragin kaka ɗaya a United a watan Yulin bara, ya ɗauki kofi huɗu a ƙungiyar da suka haɗa da FA Cup a 2016 da Community Shield da League Cup da kuma Europa League a kakar 2016-17.

Kawo yanzu manyan ‘yan wasa biyar ne a United za su bar ƙungiyar a bana da suka haɗa da Nemanja Matic da kuma Edinson Cavani, waɗanda ƙungiyar ta sanar.