Kotu ta umarci kamfanin MTN su biya diyyar miliyan 200 ga yarinya ‘yar shekara 4

Daga AMINA YUSUF ALI

Wata kotun dake zamanta a garin Damaturu ta jihar Yobe a ranar Litinin ɗin da ta gabata ta umarci hukumar kamfanin sadarwa na MTN (NELMACO) da su biya Hamsatu Abdullahi Naira miliyan 200 saboda sakaci.

Ita dai wanna yarinya mai suna Hamsatu ana zargin cewa, ta rasa hannayenta guda biyu da kuma ƙafa guda a sakamakon shokin ɗin wutar lantarki daga wayoyin kamfanin MTN.

Alƙalin kotun Mai Shari’a M. Lawu Lawan ya bayyana cewa, waɗanda ake zargin, wato (MTN) sun riga sun amsa laifinsu a baki da kuma a rubuce kasancewar akwai shaidu masu ƙarfi da suka tabbatar da cewa suna da hannu a laifin da ake tuhumar su.

Alqali ya ƙara da cewa: “Hakazalika na yanke hukuncin cewa, mai ƙarar tana da haƙƙi a wajen wanda ake ƙara, a matsayin diyya saboda asarar da aka janyo mata ta naƙasar din-din-din ta hanyar rashin hannayenta biyu da ƙafarta ta dama”.

Kuma hakan a cewar sa ya jawo mata raɗaɗi mai tsanani, biyan kuɗin asibiti, firgici, da tashin hankali da kuma asarar dukiyarta duk a dalilin abinda ya faru.

Don haka a cewar sa, aka umarci wanda ake ƙarar da ya biya Naira miliyan 200 domin rage wa mai ƙarar raɗaɗin rayuwa.

Da ma tun da fari lauyan mai ƙarar, Mista Ahmed Igoche ya bayyana cewa, mai qarar ta haɗu da jan wuta ne sakamakon sakaci daga ɓangaren waɗanda ake ƙarar.

Inda ya ƙara da cewa, waɗanda ake ƙarar sun gina wata eriya ta kamfanin MTN ta biyo ta ƙofar gidan su yarinyar tare da wasu wayoyi tsirara ba kariya. A cewar sa waɗannan wayoyi su ne suka ja yarinyar mai shekara 4 inji shi.

A cewar sa wannan aiki na ganganci shi ya jawo yanke hannayen yarinyar biyu da kuma ƙafarta ta dama.