Ina alfahari da Super Eagles duk da rashin nasara a hannun Mexico – Peseiro

Jose Peseiro, sabon kocin Super Eagles, ya bayyana cewa, yana alfahari da ƙungiyar duk da rashin nasarar da suka yi a hannun Mexico da ci 2-1 a wasan sada zumunci da sanyin safiyar Lahadi.

Har ila yau ‘yan wasan na Portugal sun yaba wa ’yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NPFL), saboda rawar da suka taka a wasan.

“Ko da ya ke ba mu yi nasara ba a daren jiya, ina matuƙar alfahari da yaran,” Peseiro ya rubuta a shafin sa na twitter.

“Ƙungiyar ta nuna hali da juriya. Magana ta musamman ga ’yan wasan NPFL huɗu da suka sami damar fara wasa tare da tawagar ƙasar.”

A halin da ake ciki, ’yan wasan da ke gida da suka samu nasarar farko a ƙungiyar sun haɗa da Sani Faisal na Katsina United da Victor Mbaoma na Enyimba International FC da Chiamaka Madu da kuma Ishaq Rafiu dukkansu na Rivers United.