Shinkafa mai inganci ta ƙasar Sin ta bada gudunmuwa wajen ƙara yawan shinkafa a Nijeriya

Daga CMG HAUSA

A yayin wani taron da aka gudanar a ranar 2 ga wata dangane da taimakawa ƙasashen yammacin Afirka kafa wani tsarin noman shinkafa, Wang Xuemin, mai taimakawa babban darektan kamfanin Green Agriculture West Africa wato GAWAL ƙarƙashin shugabancin kamfanin CGCOC kuma masanin ilmin noman shinkafa, ya yi ƙarin bayani kan yawan shinkafar da ake girbewa bisa mabambantan fasahohin noma da kuma amfani da mabambantan irin shinkafa a wasu gonaki.

A shekarun baya, gwamnatin Najeriya ta bada muhimmanci kan noman shinkafa a ƙasar, ta kara zuba jari da taimakawa masana’antun shinkafa ta fuskar manufofi, sa’an nan ta mai da hankali kan haɗin gwiwa da ƙasashen duniya a fannoni masu ruwa da tsaki. Dakta Olusegun Ojo, darektan kwamitin kula da irin da ake amfani da shi a aikin gona na Najeriya ya bayyana cewa, abun da ya gani a yayin taron ya burge shi sosai. Ya ce yanzu haka ƙasarsa ta Najeriya tana neman ƙara samun shinkafa ta hanyar noma mai inganci.

A nasa ɓangare, Shehun malami Bello Zaki Abubakar, shugaban sashen haɓaka harkokin kwamitin nazarin aikin gona na Najeriya, yana ganin cewa, ƙasashen Najeriya da Sin sun samu sakamakon da dama a fannin yin haɗin gwiwar aikin gona.

Fassarawa: Tasallah Yuan