Ƙasar Sin ta bayyana ayyukan da ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 za su yi a sararin samaniya

Daga CMG HAUSA

Hukumar kula da kumbuna ta ƙasar Sin, ta ce ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 da za a tura, za su kammala aikin ginin cibiyar binciken sararin samaniya ta Tiangong, wanda ya kunshi muhimman ɓangarori 3, wadanda suka haɗa da babban ɓangaren cibiyar na Tianhe da kumbunan ɗakunan gwaji na Wentian da Mengtian.

A cewar mataimakin daraktan hukumar, Lin Xiqiang, ‘yan sama jannatin za su yi aikin gina cibiyar ta sararin samaniya zuwa ɗakin gwaje- waje na ƙasar a sararin samaniya.

ƙasar Sin ta shirya harba kumbon Shenzhou-14 ne a gobe Lahadi, daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan, inda za a tura ‘yan sama jannati 3 zuwa cibiyar ta sararin samaniya na tsawon watanni 6.

‘Yan sama jannatin na kumbon Shenzhou-14, za su yi aiki tare da takwarorinsu dake doron duniya, domin kammala haɗewa da ayyukan kumbunan dakunan gwaje-gwajen biyu da babban ɓangaren cibiyar binciken sararin samaniya.

Mai fassara: Fa’iza Mustapha