Daga CMG HAUSA
Masanin ilmin muhalli na ƙasar Zimbabwe, Courage Tavenhave ya yabawa matakan da ƙasar Sin take ɗauka na raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar ƙasa da kuma muhalli.
Courage Tavenhave, ya bayyana haka ne yayin da ya zanta da wakilin babban gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin CMG a baya-bayan nan, yana mai cewa, matakan ƙasar Sin na neman raya ƙasa ba tare da gurɓata muhalli ba, da kuma kyawawan fasahohinta, sun cancanci ƙasashen duniya su yi koyi da su.
Masanin ya bayyana cewa, a shekarun baya bayan nan, ƙasar Sin ta rubanya ƙoƙarinta na kara azama kan raya ƙasa ba tare da gurbata muhalli ba, inda ta samu gagarumar nasara a wannan fanni. Ya ƙara da cewa, yayin da ƙasar Sin take ƙara azama kan raya kanta ba tare da gurbata muhalli ba, tana taimakawa sauran ƙasashe, musamman ma ƙasashe masu tasowa, wajen bunƙasa makamashin da ake amfani da shi ba tare da gurɓata muhalli ba. Kuma ƙasarsa ta Zimbabwe tana ɗaya daga cikin irin waɗannan ƙasashe.
Masanin ya gode wa ƙasar Sin da ta kafa asusun hadin gwiwa tsakanin ƙasashe masu tasowa ta fuskar daidaita sauyin yanayi. A cewarsa, asusun ya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa ƙasashe masu tasowa ciki hadda ƙasar Zimbabwe, daidaita matsalar sauyin yanayi. A ganinsa, ya dace ƙasashen Zimbabwe da Sin su yi koyi da juna ta fuskar raya ƙasa ba tare da gurbata muhalli ba.
Fassarawa: Tasallah Yuan
