Daga BASHIR ISAH
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce, ba za ta ci gaba da kai ajiyar muhimman kayan aikinta a Babban Bankin Nijeriya (CBN) ba.
Shugaban INEC na ƙasa, Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan, yana mai cewa daga kan zaɓen gwamna na Jihar Ekiti, INEC ba za ta ƙara kai muhimman kayan aikinta a ajiya a CBN ba.
A cewar Yakubu, domin kauce wa samun akasin kayan zaɓe a yayin zaɓuɓɓuka masu zuwa ya sa aka ɗauki wannan mataki.
Ana ganin matakin da INEC ɗin ta ɗauka ba ya rasa nasa da bayyana ra’ayin shiga takarar da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya yi, inda ya ce zai yi takarar Shugaban Ƙasa a 2023.
Da ma dai Gwamnan CBN ya maka INEC da Babban Lauyan Ƙasa (AGF) a kotu inda ya buƙaci kotu ta hana ɓangarorin biyu katse masa hanzarin yin takarar Shugaban Ƙasa, amma daga bisani ya janye ƙarar.
Zargin ra’ayin siyasa ya mamaye CBN da INEC ta yi, ya sa ta ce ba ta gamsu da ci gaba da ajiyar muhimman kayayyakinta a Babban Bankin ba.
