‘Yar shekara huɗu ta mutu a Kano bayan faɗa wa Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano  ta tabbatar da rasuwar wata yarinya ‘yar shekara 4, mai suna Amina Abdullahi Garba bayan ta faɗa cikin rijiya da ke Ƙofar Waika, daura da Masallacin Karmawi a Ƙaramar Hukumar Ungoggo.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Yusif Abdullahi ya bayyana cewa, hukumar kashe gobara ta Ƙofar Nasarawa ce ta samu kiran waya na gaggawa da misalin ƙarfe 2:05 na rana, daga wani Alkasim Ibrahim.

Ya ci gaba da cewa da isar su, tawagar ceto ta gano cewa wata yarinya ‘yar shekara huɗu ta faɗa cikin rijiya. “Ƙarfe 14:05 Alkasim Ibrahim ya kawo mana kiran gaggawa.”

Saminu Yusif ya yi nuni da cewa, nan take tawagar ta garzaya, inda ta yi nasarar fito da yarinyar a sume kuma daga bisani jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwarta.

Ya ce, an miƙa gawar Amina ga Hakimin Ƙofar Waika, Alhaji Isma’ila Yusuf.

“An fito da wanda aka je ceto a sume kuma daga baya aka tabbatar da mutuwarta, an miƙa gawar ta ga Hakimin Ƙofar Waika, Alhaji Isma’ila Yusuf,” inji shi.