Tantancewa: 10 daga ‘yan takarar Shugaban Ƙasa na APC ba su kai bantensu ba

Daga BASHIR ISAH

Kwamitin tantance ‘yan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC, ya ce goma daga cikin ‘yan takarar ba su cancanci shiga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da zai gudana a makon gobe ba.

Shugaban kwamitin tantancewar, John Oyegun, shi ne ya bayyana haka a ranar Juma’a.

A cewar Oyegun, ‘yan takara 13 daga cikin 23 ne suka tsallake tantancewar da aka gudanar.

Shirin tantancewar ya gudana ne tsakanin Litinin a Talatar da suka gabata a Abuja.

Ana sa ran waɗanda suka tsallake tantancewar su shiga zaɓen fidda gwanin APC da jam’iyyar ta shirya gudanarwa daga 6 zuwa 8 na Yuni.