Yadda ƙasar Sin ta yi nasarar sauƙaƙa fatara da raya karkara a gomman shekaru

Daga: LAWAL SALE

Sanin kowa ne cewa Sin ƙasa ce wacce ta ɗauki yaƙi da fatara da muhimmanci, musanmman ma a yankunan karkara inda masu fama da ƙangin talauci suka fi yawa. Sin dai ƙasa ce mai tasowa da ta fi kowace girma a duniya kuma tana gaba-gaba a kan yaƙi da fatara ko kuma talauci a yayin da ta ɗauki matakai waɗanda suka sa ta kawar da ƙangin talauci daga dukkan fannoni zuwa shekarar 2020.

Wannan cimma nasara dai yana da inganci mai yawa a rayuwar jama’a, da tattalin arziki, da yanayin tsarin gudanar da mulki.

Matakan dai da aka fi ba da muhimmanci a yaki da fatara da raya karkara su ne kamar: fifita harkar noma a kasafin kuɗi na ƙasa, da tallafi ga manoma da masu fama da fatara, da bayar da bashi maras yawan riba, da cire haraji a kan manoma da kayan amfanin gona, da bada tallafi a kan kayan aikin gona da kuma saukaka biyan kuɗi daga ’yan makaranta na karkara. Ana kuma shawartar manoma da su riƙa shiga ƙungiyoyin hadin gwiwa domin samun ci gaba da kuma bunƙasa jarinsu.

A cikin hanyoyin da tsarin ya ƙunsa dai sun haɗa da zuba jari da bunƙasa ababen more rayuwa da bunƙasa fannin noma da bada tallafi, da bada basusssuka marasa kuɗin ruwa, haka kuma gwamnati na faɗakar da manyan kamfanoni da su zuba jari su hada kai da ƙananan ’yan kasuwa musamman waɗanda ke karkara. Lallai abin jinjinawa ne yadda wannan shiri ya yi nasara a kan sauƙaƙa fatara da kuma raya karkara a cikin shekaru goman da suka wuce.

A shekarun baya dai lokacin da na samu damar kai ziyara ƙasar Sin a yayin da na je wasu larduna waɗanda suka hada da Beijing, da Shanghai, da Anhui, da Jiangsu da Fujian da Shaanxi.

Abubuwan da suka fi burge ni a shirin yaƙi da fatara na ƙasar Sin a nan shi ne ƙoƙarin da samari da suka kammala karatun jami’o’i suke yi a kan wani shiri wanda aka ɗauka su domin aiki da taimakawa a kauyuka don ganin iyalai masu fatara su samu kuɗaɗen shiga ta hanyoyi da dama musamman noma, da kiwon dabbobi, da sana’o’i domin fitar da su daga ƙuncin fatara.

Wani abun burgewar kuma da na lura da shi a cikin ziyarce-ziyarce na a cikin ƙasar shi ne wato, manoma ba su biyan kuɗi a manyan hanyoyi wato “toll gate” in dai har sun dauko kayan amfanin gona. Suna wucwe ne kyauta, kuma wannan duk yana cikin tsarin tallafi da rage fatara ne.

Bugu da ƙari, a sakamakon wannan nauyi da jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar ta ɗauka, an samu cimma nasarar saukaka fatara da kuma bunƙasa yankunan karkara a gomman shekarun da suka gabata a ƙarƙashin shirin, wanda aka ayyana a taro na ƙasa na 18 na jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar a shekarar 2012.

A wannan lokaci ne aka ƙaddamar da shirin kuma aka tashi gaba ɗaya domin cimma nasarar kakkaɓe fatara wanda a ƙarshe aka yi nasarar fitar da mutanen da talaucin ya yi ma katutu fiye da miliyan 100. A nan dai ina iya cewa samar da abinci ta fannin faɗaɗa harkar noma da raya karkara ne babbar nasara domin a yau, ƙasar Sin tana ci da kanta duk da tana da yawan mutanen da ya kai biliyan 1.4, dan haka kuma ana samun ƙarin ci gaba a ƙauyuka.

A sakamakon nasarar da ƙasar Sin ta samu na cimma burinta na kawar da talauci da raya karkara, ƙasashen Afirka ma za su iya koyi da matakan da ƙasar Sin ta dauka domin sauƙaƙa fatara a ƙasashensu.

A Najeriya, a misali, gwamnati ta ɗauki irin wannan darasi a yayin da ta ɓullo da shirin bunƙasa noman shinkafa ta hanyar bayar da basussuka masu ƙaramar riba da tallafi ga manoma ta hanyar samar da kayan aikin gona da takin zamani.

Ta wannan darasi, manoma da dama sun samu ci gaba kuma ƙasar Najeriya ta samu bunƙasar tattalin arziki da kuma rage kuɗin fita da ake amfani da su wajen shigowa da shinkafar a shekarun baya.