Osinbajo ka saka baki a sako mu – Cewar ɗalibarsa da ke tsare hannun ‘yan bindiga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da ɗimbin fasinjojin da suka yi fashin jirgin ƙasa a tsakanin Abuja zuwa Kaduna, sun sake sakin wani bidiyo, mai ɗauke da wasu da ke hannun su, su na bayanin Gwamnatin Tarayya ta kai masu agaji, ta cece su daga hannun ‘yan bindigar.

Bidiyon wanda su ka saki a ranar Litinin, shi ne na biyar a jerin bidiyon da suka saki, tun bayan kama matafiyan a ranar Litinin, 28 ga Maris.

A ranar Litinin ce waɗanda ake tsare da su ɗin suka cika kwanaki 62 a hannun maharan.

Duk da gwamantin Nijeriya ta ce ta na bakin ƙoƙarin ta, har yau babu wata hoɓɓasa da za a iya tabbatar da cewa ta yi, domin ceto mutanen da ke tsare.

Cikin makon jiya ne su ka saki wata mata mai ciki, bayan ta tabbatar masu da cewa ta kusa haihuwa, kuma tiyata ake yi mata a lokacin haihuwa, ba da kan ta ta ke haihuwa ba.

A bidiyon da suka saki na ranar Litinin, an nuno maza biyar durƙushe a bayan mata uku waɗanda ke zaune a kan tanfol.

Ɗan bindiga ɗaya ɗauke da bindiga ya gabatar da su, tare da ba su umarnin su yi magana ga Gwamnatin Tarayya. Abin mamaki kuma shi ne yadda ɗan bindigar ke magana da Turanci. Amma sauran bidiyon huɗu da su ka yi magaba, duk da Hausa su ka yi.

Maryam Abubakar ta ce an kama ta tare da ‘ya’yan ta huɗu. Ta ce ‘ya’yan ta biyu a cikin huɗun ba su da lafiya.

Kamar yadda ɗan Ango Abdullahi ya yi jawabinsa, ya ce: “Suna na Sadik Ango Abdullahi. Mu na roƙon Gwamnatin Tarayya ta kawo mana ɗauki, ta cece mu. Yau kwanan mu 62 a hannun su, a cikin daji. Yawancin mu ba mu da lafiya, lamarin na ƙara taɓarɓarewa. A kawo mana ɗauki kafin mu kai ga rasa rayukan mu.”

A jawabin wadda suka yi aji ɗaya da Osinbanjo, ta ce: “Suna na Gladys, ina kira musamman ga Mataimakin Shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo. Ni ajin mu ɗaya da shi a Makarantar Lauyoyi. Mu ne ‘yan ajin 1978/79.

“Ka tuna kai kaka ne, kuma uba ne. Ka kawo mana ɗauki, yau kwanan mu 62 kuma ina da ɗa na da ke kwance yana jinya. Yanzu haka ban san halin da ya ke ciki ba,” inji ta.

Haka sauran duk su ka yi roƙo ga Gwamnatin Tarayya ta kai masu ɗauki.