Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Shugaban ƙaramar Hukumar Rano, Hon. Muhammad Wada, ya shiga sahun sauran shugabanni wajen miƙa saƙon taya murna ga tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Jagoran jam’iyyar NNPP, Injiniya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, bisa cikar sa shekaru 69 da haihuwa.
Hon. Wada ya bayyana cewa wannan rana ta zagayowar haihuwar Jagoran nasu ta yi kama da ranar babbar sallah, saboda farin cikin da al’umma ke ciki da kuma irin gudunmawar da Kwankwaso ya bayar ga ci gaban Jihar Kano da Nijeriya bakiɗaya.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a wurin taron murnar zagayowar ranar haihuwar da aka gudanar a gidajen Kwankwaso dake kan titin Mila, unguwar Bompai, a birnin Kano.
A cewarsa, da zarar Jagoran jam’iyyar NNPP ya samu damar zama shugaban ƙasar nan, “lashakka abubuwa da dama za su dawo daidai, kuma talakawa za su ji sauƙin rayuwa.”
Ya ƙara da yin addu’ar Allah ya ƙara wa Jagoran darikar Kwankwasiyya lafiya, nisan kwana mai albarka, da ƙarfafa shi a ci gaba da fafutukar ceto talakawa daga matsin tattalin arziki.
Shi ma shugaban majalisar kansiloli ta ƙaramar Hukumar Kumbotso, Hon. Rabiu Roja Mariri, ya bayyana farin cikinsu da ganin wannan rana mai albarka, inda ya bayyana Kwankwaso a matsayin uba kuma jagora na gari wanda ya yi abubuwa masu tarin yawa wajen bunƙasa rayuwar al’umma.
Roja ya ce, “Jagoranmu shugaba ne nagari, abin koyi ga kowa. Ya kamata matasa su rungumi halayen kirki irin nasa domin ganin al’umma ta cigaba.”
Ya kammala da fatan Allah ya ƙara wa Jagoran nasu albarka da samun damar ci gaba da jagorantar al’umma bisa gaskiya da adalci.
