
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani ɗalibin aji 3 a Jami’ar Bayero da ke Kano mai suna Abdullahi Hafizi ya rasu yayin da wasu ƴan ƙwacen waya suka daɓa masa wuƙa a gidansa da ke Ɗorayi Quarters a Ƙaramar Hukumar Gwale, Jihar Kano.
Lamarin, wanda ya auku da misalin ƙarfe 11 na dare, ya jefa al’umma a makarantar cikin jimami yayin da ɗalibai da malamai suke cigaba da bayyana jimaminsu a kai.
Daraktan hulɗa da jama’a na jami’ar, Lamara Garba a wata takarda ya bayyana iftila’in a matsayin babban rashi ga baki ɗaya ƴan jami’ar.
Ya ce, duk da cewa al’amarin ya faru ne a wajen farfajiyar makarantar, hukumar gudanarwarsu na cigaba da ƙoƙarin bada kulawa ga ɗaukacin ɗaliban jami’ar.
Bayan faruwar al’amarin ne aka garzaya da gawarsa zuwa mahaifarsa da ke Zariya a Jihar Kaduna inda aka yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Jami’ar ta kuma kirayi ɗalibai da su kwantar da hankali tare da sanya ido akan ababen da ke faruwa a yankunansu, tana mai kira ga al’umma da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai wajen samar musu da bayanai masu amfani.
Haka kuma, jami’ar ta yi addu’ar Allah Ya ji ƙan mamacin tare da miƙa saƙon jajenta ga iyalansa, ƴan uwa da abokan arziƙi.
