Katsina: Ƙungiya ta jajenta kisan masallata a masallacin Malumfashi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuj

Ƙungiyar Ci-gaban Malumfashi (MADA) ta jajenta wa iyalan waɗanda suka rasu a harin Masallaci da ƴan bindiga suka kai a Gidan Mantau da ke Ƙaramar Hukumar Malumfashi a jihar Katsina.Lamarin ya yi sanadin mutuwar kimanin mutane guda 50.

Shugaban ƙungiyar, Malam Salisu Bawa a wata takarda, ya bayyana saƙon ta’aziyyar a ranar Asabar.

Ya ce, suna taya iyalan waɗanda suka rasu jimami da kuma fatan samun waraka cikin lokaci ga waɗanda suka jikkata.

Bawa ya kuma yi alla-wadai da harin inda ya kirayi gwamnatin tarayya da ta ƙara baza jami’an tsaro a yankunan da ke fama da matsalolin ta’addanci a jihar domin ƙaurace wa faruwar irin haka a nan gaba.

Ya kuma bayyana kisan gillar a matsayin abinda aka yi bisa rashin imani da mugunta, yana mai kira ga hukumomi da su ruɓanya ƙoƙarinsu a yaƙi da ya bindiga.

Kazalika, ya yaba wa sojoji bisa hoɓɓasa da suka yi wajen ceto mutane 72 da aka yi garkuwa da su a yankin duwatsun Pauwa da ke Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara a jihar.

By Babaji