Kotu ta ɗage shari’ar El-Rufai zuwa watan Afrilu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Mai bai wa tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana cewa kotu ta ɗage shari’ar da ake yi da tsohon gwamnan zuwa ranar 23 ga Afrilu, 2026, bayan da aka kasa gabatar da shi a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja.

Sanarwar da ya fitar ya ce mai gabatar da ƙara ya buƙaci kotu ta ba da wa’adin makonni biyu domin bai wa jami’an DSS damar gabatar da El-Rufai wanda ke hannu hukumar ICPC.

Sai dai lauyan El-Rufai, Wole Iyamu, ya shaida wa kotu cewa babu wani uzuri da zai hana DSS gabatar da shi tun da yake yana hannun wata hukuma ta gwamnati, yana mai cewa ba sai an nemi ƙarin lokaci ba.

Daga bisani alƙalin, Mai shari’a Joyce Abdulmalik, ta amince da ɗage shari’ar har zuwa watan Afrilu, wanda a cewar Muyiwa ya zarce buƙatar da lauyoyin nasu suka nema.

Rahotanni sun nuna cewa El-Rufai yana tsare tun ranar 16 ga Fabrairu, lokacin da ya amsa gayyatar EFCC da kansa, kafin daga bisani ICPC ta karɓe shi a daren 18 ga watan, kuma har yanzu ba a ba da belinsa ba.

A gefe guda kuma ana sauraron ƙarar da El-Rufai ya shigar kotu kan tauye haƙƙinsa.

By ukarofi