Kotu ta dakatar da yin zaɓukan ƙananan hukumomi a Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mai Shari’a Simon Amobeda na Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ya dakatar da Hukumar Zaɓe (KANSIEC) daga gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomin jihar da aka shirya yi a ranar Asabar.

Alƙalin ya ce, naɗa shugaban hukumar da mambobinta da aka yi wanda a lokacin aka gan su ɗauke da allunan da ke nuna cewa su mambobin jam’iyyar NNPP ne ya ci karo da dokar ƙasa da ta zaɓen jihar.

Don haka ne kotun ta haramta wa hukumar gudanar da zaɓen tare da umartar INEC kan kar ta ba ta kayayyakin gudanar da zaɓe har sai ta bi ka’idodi da hanyoyin da doka ta tsara.

An dai ayyana ranar Asabar, 26 ga watan Oktoba, 2024 a matsayin ranar zaɓen.

By Babaji